Shugaba Tinubu Zai Halarci Taron Addu'a da Allah Ya Karɓi Rayuwar Mai Martaba Sarki

Shugaba Tinubu Zai Halarci Taron Addu'a da Allah Ya Karɓi Rayuwar Mai Martaba Sarki

  • Shugaba Bola Tinubu zai tafi jihar Ogun a ranar Lahadi mai zuwa domin halartar addu'ar takwas ta marigayi Sarkin Ijebulanda, Sikiru Adetona
  • Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 18 ga watan Yuli, 2025
  • Mai martaba Sarkin ya rasu ne ranar 13 ga watan Yuli 2025, jim kaɗan bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron addu’ar kwana takwas da rasuwar marigayi Sarkin Ijebuland, Oba Sikiru Adetona, a ranar Lahadi mai zuwa.

Bola Tinubu zai halarci taron addu'ar domin yiwa iyalin Marigayi Sarkin, gwamnatin Ogun da ɗaukacin al'ummar jihar ta'aziyya bisa wannan rashi.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Sarkin Ijebuland.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai je ta'aziyyar rasuwar Sarkin Ijebu a Ogun Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu zai tafi Ogun ranar Lahadi

A sanarwar da Onanuga ya fitar yau Juma'a, 18 ga watan Yuli, 2025, ya ce Shugaba Tinubu zai bar babbar birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi domin halartar wannan taro na addu’a.

Ana sa ran Tinubu zai haɗu da Gwamna Dapo Abiodun da sauran manyan baki a taron da za a gudanar a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode a ƙarshen makon nan.

Abin da zai kai Bola Tinubu jihar Ogun

Sanarwar ta ce:

"Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Lahadi domin halartar addu’ar kwana takwas ta marigayi Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona, GCON.
"Mai girma shugaban ƙasa zai haɗu da Gwamna Dapo Abiodun da sauran manyan baki a wajen taron addu'o'in nema wa Sarkin rahama da za a gudanar a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.
"Oba Adetona, wanda ya rasu a ranar 13 ga Yuli yana da shekaru 91, an birne shi washegari a Ijebu-Ode."

Kara karanta wannan

Yobe: Sarki ya tara malamai, sarakuna domin addu'o'i na musamman ga Buhari

Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Oba Sikiru Adetona ya rasu ne a ranar 13 ga Yuli, 2025, yana da shekaru 91 da haihuwa.

Rasuwar Buhari da Sarkin Ijebu ta girgiza Najeriya

Rasuwar Mai Martaba Sarkin ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke cikin jimamin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi.

An binne marigayin a gidansa da ke unguwar GRA, Igbeba, a garin Ijebu-Ode, Jihar Ogun.

Manyan baki, sarakuna, shugabannin siyasa da mazauna garin sun hallara a Ijebu-Ode a ranar Litinin domin karrama Sarkin da ya shafe shekaru 65 yana mulki.

Marigayi Sarkin Ijebulanda a jihar Ogun.
Tinubu zai halarci addu'ar bayan kwana 8 da rasuwar basarake a Ogun Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Babban Limamin Ijebuland, Miftaudeen Gbadegesin Ayanbadejo, ne ya jagoranci sallar jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Shugaba Tinubu bai samu halarta ba saboda alhinin rasuwar abokinsa Buhari, wannan ya sa ya shirya zuwa addu'ar takwas ranar Lahadi.

Tinubu ya je ta'aziyyar Ɗantata a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauka a jihar Kano a wata domin ta'aziyyar rasuwar fitaccen ɗan kasuwar nan mai taimako, Alhaji Aminu Ɗantata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa Kano domin yin ta'aziyya, ba a ga Ganduje a wurin tarba ba

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne suka tarbe shi a filin jirgin saman Aminu Kano.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na cikin tawagar jami’an gwamnati da suka raka Shugaba Tinubu zuwa Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262