UNIMAID: An Faɗi Babban Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Sauya Sunan Jami'a saboda Buhari
- Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ya yi magana game sauya sunan jami'ar Maiduguri saboda Muhammadu Buhari
- Alausa ya bayyana cewa an canza sunan UNIMAID don girmama gudunmawar Buhari wajen habaka ilimi a Najeriya lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023
- Ya ce wannan matakin na nuna Buhari da Bola Tinubu na ganin ilimi a matsayin tushen cigaba da ci gaban ɗan adam a kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan Ilimi, Dr. Olatunji Alausa ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan karrama marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Alausa ya ce an canza sunan Jami’ar Maiduguri zuwa 'Muhammadu Buhari University', Maiduguri saboda jajircewar marigayi shugaban wajen ci gaban ilimi.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Punch ta samu wanda ya fitar a madadin Ma’aikatar Ilimi da fannin ilimi na Najeriya.

Kara karanta wannan
'Babu kuɗi': Yadda Buhari ya roƙi gwamnoni su tara N700m kafin ya biya su daga baya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya karrama Buhari bayan sauya sunan jami'a
Shugaban kasa ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na musamman da jinjina ga rayuwa da hidimar marigayi Buhari, yana mai fadin rawar da ya taka a fannin tsaro da yaki da rashawa.
Shugabanni da dama sun halarta ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, gwamnoni da ministoci.
A cewar sanarwar, Shugaban kasa ya gabatar da bukatar sauya sunan jami’ar Maiduguri don karrama gudunmawar Buhari, kuma majalisar ta amince da hakan.

Source: Twitter
UNIMAID: Ma'aikatar ilimi ta yabawa Tinubu
Alausa ya ce sun karɓi wannan girmamawa da kima daga gwamnatin tarayya da godiya duba da haɓakar ilimi a mulkin Buhari.
Daraktar yada labarai da hulɗa da jama’a, Folasade Boriowo ta ce Tinubu ne ya bayyana hakan a zaman musamman na majalisar zartarwa.
Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Buhari (2015–2023) ta kafa muhimman tsare-tsare kamar Anchor Borrowers’ Programme, TSA, ERGP, da shirin agajin zamantakewa.
Ya kara da cewa:
“Ma’aikatar Ilimi na cike da godiya saboda an zabi bangaren a matsayin hanyar da za a kafa tarihin marigayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
“Matakin Shugaba Tinubu na nuna kauna da girmamawa, yana nuna yadda yake da yakinin cewa ilimi shi ne ginshikin gina kasa da kuma ɗan Adam."
'Tinubu yana daraja ilimi a Najeriya' - Minista
Ministan ilimi ya ce wannan alama tana nuna yadda gwamnatin Tinubu ke daraja ilimi a matsayin muhimmin ginshiki ga cigaba da cigaban al’umma.
Sanarwar ta jaddada cewa Ma’aikatar Ilimi za ta ci gaba da kare dabi’un hidima, gaskiya da kwarewa da Buhari da Tinubu suka wakilta, Tribune ta ruwaito.
Legit Hausa ta yi magana da dalibin UNIMAID
An yi ta ce-ce-ku-ce bayan sauya sunan jami'ar inda mafi yawa ke sukar matakin da Tinubu ya dauka.
Wani dalilibi a tsangayar tattalin arziki, Khalil Adam ya ce abin bai masa dadi ba ko kaɗan.
Ya ce:
"Dalibai da wasu malamai da dama sun soki matakin duba da shura da sunan UNIMAID ta yi a fadin Najeriya."
Khalil ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba kan lamarin yayin da kungiyar ASUU da tsofaffin dalibai suka yi korafi kan haka.
Yusuf Buhari ya yiwa Tinubu godiya
Kun ji cewa an gudanar da taron majalisar zartarwa na musamman a Abuja saboda marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ɗan tsohon shugaban kasa ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa mutunta mahaifinsa, Muhammadu Buhari da jana’iza ta kasa da aka shirya.
Yusuf Buhari ya yaba da goyon bayan gwamnati, Majalisa, gwamnoni da 'yan Najeriya da suka jajanta musu tare da halartar jana’izar da aka yi a Daura.
Asali: Legit.ng

