Malami Ya Shawarci Iyalan Buhari, Ya ce Yan Najeriya na da Hakki a Dukiyarsu
- Malamin addinin Muslunci, Usman Hamza Al-Bayan ya shawarci iyalai da masoyan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- Ya ce akwai masu safarar shinkafa da tsohon shugaban ya ba da umarnin a harbe da ma wasu da gwamnatinsa ta jefa a wahala
- Malamin ya ce saboda ire-iren waɗannan, akwai bukatar su taru wajen nema masa gafara ta hanyar samar da gidauniyar Muhammadu Buhari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Malamin addinin Musulunci, Malam Usman Hamza Al-Bayan, ya shawarci iyalan tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Malamin ya bayyana cewa akwai hanyoyi da dama da iyalan tsohon shugaban za su nema masa gafara da rahamar Allah (SWT).

Source: Twitter
A bidiyon da Al Bayan Online TV ta wallafa a shafin Facebook, akwai hanyoyi da matarsa A'isha Buhari da ’ya’yansa za su bi domin neman rahama ga marigayin.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarar malamin ga iyalan Buhari
Sawaba Online ta wallafa bidiyo a shafin Facebook inda Malamin Usman Hamza Al-Bayan ya bayyana cewa talakawan Najeriya na da haƙƙi a dukiyar iyalan Buhari.
Malamin ya ce:
“Daga cikin abin da za ku yi – Allah Ya tausaya maku, Ya tausaya masa – shi ne ku buɗe gidauniya ta jin ƙai ga al’umma.”
“A mulkin Babanku, mawadata da 'yan kasuwa sun karairaye, sun talauce. Wanda bai gaya muku haka ba, ya ha’ince ku, karya yake muku.”
Ya ce a zamanin Buhari yana shugaban kasa, akwai mutane da dama da aka kashe su saboda safarar shinkafa bisa umarnin shugaban.
"Talakawa suka tara wa Buhari kuɗi," Malami
Malamin ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi mulki ne da dukiyar talakawa da suka rika tara masa tun yana neman takara.
Ya ce a lokacin da ’yan Najeriya suka rika mara masa baya, babu wanda ke da wani arzikin a zo a gani daga cikin iyalansa.

Kara karanta wannan
An fara fito da bayanai kan 'cabal', Gambari ya fallasa yadda aka mamaye gwamnatin Buhari

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa:
“Kai Yusuf Buhari, an yi lokacin da daga cikin ’ya’yan shugabannin Afirka, ba wanda ya kai ka arziki. Talakawa ne suka tarawa babanka kuɗi har ya kai ga yin takara.”
Malamin ya jaddada cewa dole ne ’ya ’yan shugaban da sauran iyalansa su haɗa kai wajen bayar da sadaka, musamman ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
A cewarsa, wasu sun talauce a lokacin Buhari, yayin da wasu kuma suka tara dukiya, saboda haka akwai buƙatar su cire wani kaso daga cikin abin da suka samu don taimakawa talakawa.
Malami ya magantu kan dukiyar magada Buhari
Malam Murtala Ahmad, Malamin addinin Musulunci ne a Kano, ya kuma ce wanda ya tara dukiya Allah ke yi wa hisabi a kai.
"Wanda ya tara, shi Allah zai yi wa hisabi. To amma malamin da ya ce ƴan Najeriya suna da haƙƙi a dukiyar da ƴaƴan Muhammadu Buhari suka gada, to wAllahu a'alamu."

Kara karanta wannan
'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients
"Ban san hujjar da ya dogara da ita, ya fadi haka ba."
Ya ce amma idan yaran Marigayin sun san wata dukiya da ya tara ta haramtacciyar hanya, sai su mayar wa mai ita.
"Amma idan suna da yaƙinin cewa dukiyar da ya mallaka ta halal ce, sun ci halal."
Kalaman da Buhari ya yi wa shugaban majalisa
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya bayyana irin nasiha da marigayi tsohon shugaban ƙasa, ya yi masa.
Tajudeen ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron Majalisar Zartarwa ta Musamman (FEC) da aka shirya domin girmama rayuwar Muhammadu Buhari.
Ya ce bayan nasararsa a zaben 2023 inda ya zama kakakin majalisar karo na huɗu, Buhari ya kira shi a Birtaniya kuma ya ba shi wata nasiha ta musamman.
Asali: Legit.ng