"Kamar Ya Sani," Kalaman da Buhari Ya Faɗa game da Mutuwarsa kafin Ya Sauka daga Mulki

"Kamar Ya Sani," Kalaman da Buhari Ya Faɗa game da Mutuwarsa kafin Ya Sauka daga Mulki

  • Femi Adesina ya bayyana tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai ƙima da daraja kuma shugaba nagari
  • Tsohon kakakin shugaban ƙasar ya ce Buhari ya taɓa faɗa cewa bayan ya bar mulki, zai koma gida ya jira lokacin da Allah kira shi
  • Ya ce ya kai wa Buhari ziyara bayan ya dawo gidansa na Kaduna daga Daura, yana mai cewa ita ce haɗuwarsu ta ƙarshe kafin ya tafi Landan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Tsohon kakakin shugaban ƙasa, Femi Adesina ya tuna tattaunawarsa da Marigayi Muhammadu Buhari watanni ƙalilan kafin karewar wa'adinsa na biyu a mulki.

Adesina ya ce wasu na mamakin yadda mutuwar dattijo ɗan shekara 82 ta girgiza su, yana mai cewa Buhari shugaba ne na gari da zai wahala a samu kamarsa.

Kara karanta wannan

Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali

Marigayi Muhammadu Buhari da Femi Adesina.
Femi Adesina ya tuna yadda Buhari ke tunawa da mutuwa a rayuwarsa Hoto: @FemiAdesina
Source: Facebook

A wani rahoto da Tribune Nigera ta wallafa, Adesina ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin jarumin soja, shugaba nagari, kuma mutum mai kima da daraja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ko kaɗan bai taɓa tunanin Buhari zai rasu daga nan zuwa shekaru 10 masu zuwa ba bayan sauka daga mulki a 2023.

Haɗuwar Femi Adesina da Buhari ta ƙarshe

Tsohon hadimin shugaban ƙasar ya ce haɗuwarsa ta ƙarshe da Shugaba Buhari ita ce lokacin da ya kai masa ziyara gidansa na Kaduna, wanda aka gyara masa a kwanakin baya.

Ya ce a ziyarar da ya kai masa a watan Maris, 2025, ya same shi yana karanta jaridun ƙasa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Femi Adesina ya ce ya haɗu da Buhari a lokacin watan Ramadan, ranar 10 ga watan Maris, kuma sun yi buɗa baki tare da shi da uwargidansa, Hajiya Aisha Buhari.

A cewarsa, daga wannan rana ba su sake haɗuwa ba domin ya tafi Landan a duba lafiyarsa kamar yadda aka saba, amma sai dai gawarsa aka dawo da ita.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari ta sa jigo a APC ya yi nasiha mai ratsa zuciya ga shugabanni

Abin da Buhari ya faɗa game da mutuwarsa

Adesina ya ce ba zai taɓa manta lokacin da ya shafe tare da tare da Baba Buhari, wanda ya kira ubangida, aboki kuma shugaba.

"A ranar Talata, 15 ga Yuli, aka dawo da gawarsa gida domin binne shi, bayan rasuwarsa da kwanaki biyu. Na kalli kabarin da aka haka a wuri na musamman da yake yawan zama a cikin harabar gidansa.
"Na tuna da wani abu da Buhari ya fada min a ranar 30 ga Maris, 2023, kwanaki 60 kafin mu bar ofis. Na tambaye shi, shugaba me za ka yi bayan barin Ofis?
"Amsar da ya ba ni ita ce, 'A yanzu ina fatan barin wannan wuri, daga nan kuma za mu jira mutuwa, zan tafi ƙabarina idan lokaci na ya yi."

- Femi Adesina.

Muhammadu Buhari
Femi Adesina ya ce Buhari ya gaya masa bayan barin mulki, sai kabari Hoto: @GarShehu
Source: Twitter

Yusuf Buhari ya godewa Shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ɗan tsohon shugaban kasa ya gode wa Bola Tinubu bisa mutunta mahaifinsa, Muhammadu Buhari da jana’iza ta kasa.

Kara karanta wannan

Diyar Buhari, Hadiza ta fadi tafarkin da mahaifinta ya dora yaransa a kai

Yusuf Buhari ya miƙa wannan godiya a madadin iyalan Buhari a wurin taron Majalisar zartarwa da aka shirya musamman domin karrama marigayin.

Ya kuma gode wa Majalisar Tarayya, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, sauran gwamnoni da ’yan Najeriya bisa kasancewa tare da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262