An Kutsa Gidan Buhari, an Samo yadda Ya Yi Wata Irin Rayuwa da Iyalansa

An Kutsa Gidan Buhari, an Samo yadda Ya Yi Wata Irin Rayuwa da Iyalansa

  • Iyalan marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana yadda ya rayu a gida cikin natsuwa da soyayya ga 'ya'yansa
  • Sun bayyana cewa Muhammadu Buhari ya kasance mai son gaskiya da hana cin amana tun daga ƙuruciyar ’ya’yansa
  • Iyalan tsohon shugaban kasar sun gode wa ‘yan Najeriya da suka yafe masa, suna masu cewa yana da niyyar alheri ga ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kastina - Yayin da Najeriya ke ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, iyalansa sun bayyana wasu sirrika da suka shafi rayuwarsa a gida.

Buhari ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin London, bayan doguwar rashin lafiya da ba a bayyana ba, sannan aka dawo da gawarsa aka birne shi a Daura ranar Talata.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba: Dattijon Arewa ya tsage gaskiya kan 'kurakuran' Buhari

Shugaba Buhari tare da iyalan shi a fadar shugaban kasa
Shugaba Buhari tare da iyalan shi a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Iyalan, ciki har da 'ya’ya da jikokinsa, sun yi magana da BBC Hausa, inda suka bayyana halayensa na barkwanci, koyar da ladabi da kiyaye gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rayuwar Buhari a gida cikin iyalan shi

Daily Trust ta wallafa cewa Hadiza Muhammadu Buhari ta fadi yadda ya horar da su kan gaskiya da kada su taɓa abin da ba nasu ba, duk da ƙanƙantar shekarunsu.

Ta kara da cewa ya kasance mai horar da yara cikin tsari da bin doka, yana da ƙa’ida da bai yarda da cin hanci ko yaudara ba, har ma a cikin gida.

Rayuwar Buhari tsakanin ‘ya’ya da jikoki

Jikar shi ta ce duk da tsaurin da ake gani yana da shi, Buhari ya kasance mai sauƙin kai da soyayya ga iyalansa, inda ya ke ba su laƙabi na musamman da kuma yawan dariya da hira da su.

Ta kara da cewa ya kasance yana da kusanci da jikokinsa sosai, har yana ba su sunaye na musamman da ke nuna ƙauna da ƙayatarwa.

Kara karanta wannan

'Shehu Dahiru Bauchi bai yarda Inyass na bayyana a jikin bango ko sama ba,'

Hadiza ta ce Buhari yana yawan tunawa da mahaifiyarsa, kuma yana danganta hakan da 'yarsa ta musamman, yana gaya mata cewa tana kama da mahaifiyarsa.

Buhari na son dabbobi a cikin gidansa

Wata jikar shi ta ce ya kasance mai son dabbobi kamar shanu, kunkuru da kuma tantabara, kuma yana da al’adar ba wa jikokinsa dabbobi don su riƙa kiwon su tun suna ƙanana.

Wani mai mika masa abinci ya ce dankalin turawa da kwai, da shayi Buhari ya ci kafin tafiya London jinya.

Ma’aikatan gidan Buhari sun bayyana shi a matsayin mutum mai sauƙin kai da son zaman lafiya da mutunta su a ko da yaushe.

Sun ce ya kasance mai yawan tambayarsu lafiyarsu, yana jawo su kusa da nuna musu soyayya da kulawa, ba tare da nuna fifiko ko girman kai ba.

Iyalan Buhari sun yi godiya ga ‘yan Najeriya

Hanan Buhari ta ce suna mika godiyarsu ga ‘yan Najeriya da suka nuna yafiya da juyayi bayan rasuwarsa.

Buhari da wasu daga cikin 'ya'yan shi
Buhari da wasu daga cikin 'ya'yan shi. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Ta ce bai da wata manufa sai ta gina ƙasa, kuma ya kasance mai fatan alheri a duk lokacin da ya ke jagoranci, duk da matsin lamba da ya fuskanta.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari 3 da har yanzu suke tayar da jijiyoyin wuya duk da Allah ya masa rasuwa

Malamai sun yi wa Buhari addu'a

A wani rahoton, kun ji cewa malaman addinin Musulunci daban daban sun ziyarci gidan shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jagoranci tawagar kungiyar Izala domin yi wa iyalan marigayin ta'aziyya.

A daya bangaren, shugaban majalisar malaman Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ziyarci gidan Buhari a Daura.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng