Abin da Yusuf Buhari Ya Faɗawa Tinubu cikin Hawaye a Taron Majalisar Zartarwa
- Ɗan tsohon shugaban kasa ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa mutunta mahaifinsa, Muhammadu Buhari da jana’iza ta kasa da aka shirya
- Yusuf Buhari ya yaba da goyon bayan gwamnati, Majalisa, gwamnoni da 'yan Najeriya da suka jajanta musu tare da halartar jana’izar da aka yi a Daura
- Ya fadi hakan yayin taron majalisar zartarwa na musamman da aka shirya saboda marigayin a birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ɗan tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi jawabi yayin taron majalisar zartarwa ta musamman a Abuja da aka shirya.
Yusuf Buhari ya nuna godiya ga Shugaba Bola Tinubu saboda girmama mahaifinsa da jana’izar da ta dace da matsayinsa da aka gudanar a ranar Talata.

Asali: Twitter
Yusuf Buhari ya yi godiya ta musamman ga Tinubu

Kara karanta wannan
'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients
Ya bayyana haka ne a wani taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da aka fadada wanda aka shirya don girmama Buhari a Abuja ranar Alhamis, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan Buhari, wanda ya halarci zaman na musamman tare da ’yan uwansa, ya gode wa Shugaba Tinubu da gwamnatinsa bisa goyon bayan da suka ba mahaifinsa da iyalinsa.
Ya kuma gode wa Majalisar Tarayya, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, sauran gwamnoni da ’yan Najeriya bisa kasancewa tare da su.
Yusuf ya ce:
“Ya nuna cewa an daukaka shi (Buhari) fiye da ɗan siyasa, an ɗaukaka shi a matsayin aboki kuma uba.
“Ga dukkan mambobin Majalisar Zartarwa, saboda kulawa da jana’izar da kuka yi wa mahaifinmu, muna matuƙar godiya.
“Ina kuma son gode wa Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai, da dukkan mambobin Majalisar Tarayya saboda girmamawa da kuka nuna masa a Daura.

Asali: Twitter
Yusuf Buhari ya zubar da hawaye a gaban Tinubu
Yusuf Buhari ya ce ba zai manta da abin da aka yiwa iyalansu ba kama daga ziyarce-ziyarce zuwa addu'o'i da ake ta yi musu.
Ya yi addu'ar Allah ya albarka ce su gaba daya yayin da yake zubar da hawaye saboda karamci da aka nuna musu.
Ya kara da cewa:
“Ziyararku, kiranku da addu’o’inku sun zama babban girmamawa ga mahaifinmu, muna godiya matuƙa da goyon baya da jituwa da kuka nuna.
“Allah ya albarkace mu gaba ɗaya, Nagode Baba. Nagode baba. Nagode baba.
“Allah ya ci gaba da yi maka albarka, ya ba ka arziki, ya kare ka a duk tsawon wa’adinka.”
Har ila yau, matashi mai amfani da kafar sadarwa, Imran Muhammad ya wallafa faifan bidiyon Yusuf yayin jawabinsa a manhajar X.
Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari
A baya, mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa 'Muhammadu Buhari University', a domin girmamawa shi.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
Tinubu ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, wanda bai yarda da son rai a harkokin siyasarsa ba ko kadan inda ya bar tarihi.
Shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kafa tsari na gaskiya da rikon gaskiya da zai ci gaba da zama madubi ga shugabannin gaba duba da darussan da za a kwasa.
Asali: Legit.ng