Malaman Musulunci da Kiristoci Sun Taru a Daura, An Taru don Rokawa Buhari Rahama
- Har yanzu tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na ci gaba da samun ruwan addu'o'in neman rahama da jin kai
- Fitattun malamai Musulmi da Kiristoci sun gudanar da addu’o’in neman rahama a Daura inda aka roki Allah ya gafarta wa Buhari
- Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai fitattun malaman addinin Musulunci da na Kirista a ciki da wajen jihar Katsina
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fitattun malaman addinin Musulunci da na Kirista tare da manyan jami’an gwamnati sun taru a garin Daura, Jihar Katsina, a ranar Alhamis.
An haɗu ne domin gudanar da addu’o’in neman rahama da afuwar Allah Subhanahu Wata'ala ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa an gudanar da zaman addu’ar ne a gidan marigayin, bayan addu’o’in Fidau na kwana uku da aka yi a ranar Laraba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musulmi, Kiristoci sun yi wa Buhari addu'a
This day ta wallafa cewa daga cikin malamai da suka halarci taron akwai Shugaban ƙasa na Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah, Sheikh Bala Lau.
Sai kuma Sheikh Sani Yahaya Jingir; Sheikh Kabiru Gombe; Sheikh Ali Pantami da kuma Bishof Gerald Musa, wanda shi ne Bishof na cocin Katolika na Katsina.
Haka zalika, Sarakunan gargajiya kamar Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman, da Sarkin Daura, Dr Faruk Umar Faruk, da wasu sarakuna na gargajiya sun samu halarta.
Abin da malamai ke fadi kan Buhari
Sheikh Bala Lau ya bayyana Buhari a matsayin mutumin kirki, yana mai cewa marigayin ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban Najeriya.
Sheikh Isa Ali Pantami, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, ya ja hankalin Musulmi da su ci gaba da yi wa Buhari addu’a kullum, kamar yadda Alkur’ani ya shar’anta.
Ya ce:
“Addu’a ga Babanmu, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bai kamata a takaita ta ga kwanaki uku ko bakwai kawai ba.
“A Musulunci, ba a iyakance lokacin addu’a ga mamaci, har abada ake yi. Don haka nake roƙon kowa da ya sanya shi cikin addu’o’insa na yau da kullum."
Bishof Musa ya yabi Buhari
A nasa jawabin, Bishof Gerald Musa ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai ladabi da kame kai, wanda ya rayu da ɗabi’ar da ya kamata shugabanni su kwaikwaya.

Source: Twitter
Ya ce:
“Na koyi abubuwa da dama daga Buhari tun yana raye. Yana da gaskiya musamman a lokacin mulkinsa na soja."
“Ina tuna yadda a matsayin ɗalibi muka yi sha’awar manufofinsa, musamman yakin da ya yi da rashin da'a.”
"Dan adam tara ya ke, bai cika goma, amma Buhari ya bar baya mai kyau. Muna rokon Allah ya saka masa da alheri kuma ya gafarta masa.”
'Yan majalisa sun yi ta'aziyyar Buhari
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jagoranci tawagar manyan ‘yan majalisar dokokin tarayya zuwa garin Daura.
A yayin jawabi a gidan gwamnati, Akpabio ya bayyana marigayi Buhari a matsayin gwarzon jagora, wanda ya ya rayu a cikin gaskiya da rikon amana.
Ya ce Buhari ya yi wa Najeriya hidima tun daga lokacin da ya ke zamanin soja har zuwa lokacin da aka zabe shi shugaban kasa a tsarin dimokuraɗiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

