Kogi: Tsohon Gwamna, Yahaya Bello Ya Ƙara Aure a Wani Bidiyo, Ya Rufe Ƙofa
- An tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya angwance a bikin da aka gudanar a Abuja
- Yahaya Bello ya angwance ne a karo na hudu a Abuja da matarsa, Hiqma a wani bikin sirri da danginsa da abokai suka halarta
- Matarsa ta uku, Hafiza, ta tabbatar da auren a kafar sadarwa, inda ta yi maraba da sabuwar amarya tare da addu’ar albarka da zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya kara aure.
Yahaya Bello ya angwance ne a birnin Abuja a karshen makon da ya wuce wanda hakan ke tabbatar da cewa ya rufe kofa.

Source: Facebook
Matarsa ta uku, Hafiza Yahaya Bello ita ta tabbatar da auren a shafin Instagram inda ta yi maraba da sabuwar amarya tare da bayyana farin cikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin Yahaya Bello da badakalar N80.2bn
An gudanar da wannan biki ne yayin da ake cigaba da tuhumar Yahaya Bello kan badakalar makudan kudi lokacin mulkinsa.
Tun bayan sauka daga madafun iko, hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ke tuhumar tsohon gwamnan kan zargin badakalar fiye da N80bn.
Hukumar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan na son kawo cikas a shari'arsa da ke yi kan zargin wawure makudan kudi.
A zaman kotun da ke gudana, EFCC ta ce jami'an tsaron Yahaya Bello sun yi barazana ga daya daga cikin shaidunsu da ke aiki a wani bankin Najeriya.

Source: Facebook
Yahaya Bello ya kara mata ta 4
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kara aure karo na hudu da Hiqma Yahaya Bello a wani biki na sirri da aka gudanar a Abuja.
Bikin auren ya samu halartar 'yan uwa da abokai na kusa, kuma an gudanar da shi cikin yanayi na kamewa da rashin nuna shi a fili.
Matarsa ta uku ta ce:
“Alhamdulillah, iyalinmu ya kara girma da kauna! Maraba da sabuwar mamba, Mrs. Hiqma Yahaya Bello! Allah ya albarkaci zamanmu."
Bello ya yi mulki daga 2016 zuwa 2024 karkashin jam’iyyar APC, kuma an taba yi masa lakabi da matashin gwamna mafi ƙarancin shekaru a Najeriya.
Su wanene sauran matan Yahaya Bello?
Kafin wannan sabon aure, Bello na da mata uku, Amina Oyiza Bello, Rashida Bello, da Hafiza Bello, wacce ta tabbatar da sabon auren.
Duk da wadannan matsaloli na shari’a da Yahaya Bello ke fuskanta, ya ci gaba da bikin aurensa cikin sirri ba tare da wani alfahari ko bayyana shi ba.
An daura auren ɗan Yar'Adua a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa manyan 'yan siyasa a Najeriya sun taru a Babban Masallacin Abuja domin shaida daurin auren Umaru Musa Yar’Adua da Maryam Ayuba.
Daga cikin manyan baki akwai dangin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Umaru Yar’Adua da sauran abokai da ‘yan siyasa masu mutunci da dangantaka da iyalan.
An yi addu'a da roƙon Allah ya ba sababbin ma’auratan hikima da haƙuri domin gina gida mai cike da farin ciki da fahimtar juna.
Asali: Legit.ng

