"Ka Kula da Talakawa": An Ji abin da Buhari Ya Fadawa Peter Obi kafin Ya Rasu
- Peter Obi ya kai ziyara Daura domin ta’aziyyar Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana shi a matsayin shugaban da ya damu da talakawa
- Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar LP a 2023, ya tuno haduwarsa da Buhari, wanda ya ce ba bar masa wasiyyar kula da 'yan kasar
- Obi ya ce har yanzu yana rike da wannan wasiyya ta Buhari, kuma yana ganin tsohon shugaban kasar ya yi kokari a lokacin mulkinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Daura - 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Mista Peter Obi, ya je Daura da ke Katsina, domin ta'aziyyar marigayi Muhammadu Buhari.
Peter Obi, ya tuna wata ganawa da ya yi da marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a lokacin yakin neman zabe.

Source: Twitter
Haduwar Buhari da Obi a wajen siyasa
Yayin ziyarar tasa, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba wanda ya jajirce wajen tunkara da magance matsalolin talakawan Najeriya, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin addu’o’in kwana uku da aka shirya domin karrama marigayi Buhari.
Tsohon gwamnan ya ce ya kamata shugabanni su “koyi yadda ake yi wa kasa hidima da zuciya daya, domin wata rana za mu koma ga mahaliccinmu.”
Ya kara da cewa:
“Na samu damar ganawa da marigayi Muhammadu Buhari a lokacin da nake yakin neman zabe, kuma har yanzu ina tuna kalmominsa.
"Ya ce min: 'don Allah ka kula da talakawan Najeriya', kuma wannan shi ne abin da na fi tunawa, kuma ina ganin ya yi bakin kokarinsa yadda ya kamata.”
Dalilin Obi na makara a jana'izar Buhari
Game da abin da ‘yan Najeriya za su koya daga Buhari, Obi ya ce, “Dole mu koyi yadda ake yi wa kasar nan hidima, domin wata rana za mu koma ga mahalicci.”
A cewarsa,
“Mun shaida Buhari ya jajurce wajen da'awar taimaka wa talakawa da nuna cewa ya damu da su kuma wannan shi ne mafi dacewa da misalin mutum mai saukin kai."
Tun da fari, mun ruwaito Peter Obi ya bayyana cewa ya samu jinkirin zuwa Daura ne domin rashin jirgi da ya samu, ya ce ya gaza samun jirgin da zai kai shi Katsina.
Duk da haka, Obi ya ce wadanda suka je a ranar da ya je da wadanda suka halarci jana'iza, duka suna cikin alhinin rashin Buhari kuma suna yi masa fatan samu kyakkyawar makoma.

Source: Facebook
Rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari
Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban kasa Bola Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka karbi gawar Buhari a filin jirgin saman Katsina a ranar Talata, kafin a kai shi Daura inda aka yi jana'izarsa.
Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti da ke London bayan doguwar rashin lafiya.
Tuni aka birne shi a gidansa da ke Daura bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da dubban jama’a suka halarci jana’izarsa domin girmama tsohon shugaban kasar.
'Buhari ya hana 'yan Najeriya mutuwa'
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ce Muhammadu Buhari ya kare 'yan Najeriya daga mutuwa a lokacin da yake mulki.
Chukwuemeka Nwajiuba ya ce da gangan tsohon shugaban kasar ya ki cire tallafin man fetur, a cewarsa, da Buhari ya cire tallafin, da miliyoyin 'yan kasar sun mutu saboda tsadar rayuwa.
Tsohon ministan ya yi wadannan maganganu ne yayin da ake jimamin rasuwar Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibitin London bayan doguwar jinya.
Asali: Legit.ng


