An Rufe Majalisar Najeriya Kirif saboda Mutuwar Shugaba Buhari

An Rufe Majalisar Najeriya Kirif saboda Mutuwar Shugaba Buhari

  • Majalisun kasa ta dakatar da dukkan ayyuka har na tsawon mako guda domin girmama marigayi Muhammadu Buhari
  • Shugabannin Majalisar Dattawa da na Wakilai ne suka bada umarnin dakatar da zaman majalisa har zuwa ranar 22 ga Yuli 2025
  • Baya ga haka, majalisun sun mika ta'aziyya ga iyalan Buhari da gwamnatin Najeriya bisa rashin tsohon shugaban kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar Dokoki ta Tarayya ta dakatar da duk ayyukanta na doka na tsawon mako guda domin girmama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025 a birnin London na kasar Birtaniya yana da shekara 82.

Buhari yana addu'a a fadar shugaban kasa
Buhari yana addu'a a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Hon. Kamoru Ogunlana ne ya fitar da sanarwar hakan a ranar Litinin da ta wuce.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi babbar girmamawar da ta rage Tinubu ya yi wa Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rufe majalisa saboda makokin Buhari

Hon. Kamoru Ogunlana ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne domin bai wa 'yan majalisa damar halartar jerin ayyukan jana’izar Buhari.

A cewar sanarwar:

“Majalisar Tarayya ta Najeriya na cikin jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, GCFR, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
“Don girmama tarihin sa da hidimar da ya bayar wa kasa, shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilai sun umarci a dakatar da duk ayyukan majalisa har zuwa ranar Talata, 22 gaYuli, 2025.”

Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta ci gaba da cewa:

“An bukaci dukkan ‘yan majalisa su sake tsara ayyukansu domin samun damar halartar jana’izar marigayi shugaba Muhammadu Buhari.”

Majalisa ta yi ta'aziyya ga iyalan Buhari

Hon. Kamoru Ogunlana ya bayyana cewa shugabannin majalisar biyu na mika ta’aziyyar su a madadin dukkan ‘yan majalisa da ma’aikatan majalisa ga gwamnati da al’ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Amurka ta rufe ofishinta a Abuja, Saudiya ta aiko da sako Najeriya

Ta’aziyyar ta kuma shafi gwamnatin jihar Katsina da kuma iyalan marigayi shugaban, ciki har da matar sa da ‘ya’yansa.

Sanarwar ta ce:

“Za a ci gaba da tuna Muhammadu Buhari saboda kishinsa ga hadin kan Najeriya da kuma tsantsar gaskiyar sa a harkokin gwamnati.
“Allah Madaukaki ya gafarta masa ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus.”

Wannan matakin na Majalisa na zuwa ne bayan wasu hukumomi na gwamnati sun fara girmama marigayi Buhari, ciki har da kasa da tutoci da bude rajistar ta'aziyya.

Shugaba Bola Tinubu na jawabi ga 'yan majalisar kasa a Abuja.
Shugaba Bola Tinubu na jawabi ga 'yan majalisar kasa a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A baya dai, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati su bude rajistar ta’aziyya domin bai wa jama’a damar yin jaje.

Har ila yau, ana ci gaba da gudanar da addu’o’i a sassa daban-daban na kasar domin rokon Allah ya gafarta wa tsohon shugaban kasar.

An yi jimamin rasuwar Buhari a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa al'ummar Arewacin Najeriya sun yi jimamin rasuwar shugaba Muhammadu Buhari.

Legit ta gano cewa an yi wa tsohon shugaban kasar sallar gawa daga nesa a jihohin Filato da Gombe.

Baya ga haka, an shirya taron addu'o'i na musamman a jihohin Bauchi, Yobe da wasu sassan Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng