An Yi wa Buhari Sallar Jana'iza a Gombe yayin da ake Jiran Gawar Shi a Daura
- Daruruwan Musulmai sun gudanar da sallar gawa daga nesa ga marigayi Muhammadu Buhari a Filin ajiye motoci na Pantami, Gombe
- Sallar Salatul Ghaib ta gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a yau Talata, kafin a birne tsohon shugaban kasar a Daura
- Mahalarta jana'izar sun bayyana cewa addu’a ce ta karshe da suka yi domin roƙon gafara da rahamar Allah ga marigayin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Musulmai da dama sun taru a filin ajiye motoci na Pantami da ke Gombe domin gudanar da sallar gawa daga nesa, wato Salatul Ghaib, ga shugaba Muhammadu Buhari
Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin yi wa marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, jana'iza a Daura, jihar Katsina.

Source: Facebook
Wani mazaunin jihar Gombe, Alhaji Aminu Malam ya wallafa yadda aka gudanar da jana'izar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sallar ta gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a wani fili da ke tsakanin Filin wasan Pantami da caji ofis din ‘yan sanda na Pantami.
Hakan na zuwa ne bayan Daily Trust ta wallafa cewa an yi irin wannan sallar a jihar Filato a jiya Litinin ga shugaba Buhari.
Mahalarta sallar sun bayyana cewa hakan na daga cikin al’adun Musulunci domin nuna alhini da roƙon rahamar Allah ga mamacin, musamman idan ya rasu a wani wuri dabam.
Dalilin yi wa Buhari jana'iza a Gombe
Wani daga cikin mahalarta sallar, Muhammad Ibrahim, ya ce an shirya sallar ne domin nuna ƙauna ga marigayin shugaba Buhari, kuma domin roƙon Allah ya gafarta masa.
“Mun taru ne a nan Pantami domin yi wa marigayi Buhari sallar gawa daga nesa.
"Kowa ya san cewa yana da matsayi a tarihin Najeriya. Don haka muna roƙon Allah ya masa rahama,”
Muhammad ya kara da cewa:
“Sallar Salatul Ghaib ba sabon abu ba ne, musamman idan musulmi ya rasu a wani wuri dabam.
"Wannan hanya ce da Musulmai ke amfani da ita wajen taya ‘yan’uwansu addu’a ko da kuwa ba su samu halartar jana’izar kai tsaye ba,”

Source: Facebook
Matasan Gombe sun halarci jana'izar Buhari
Taron sallar ya jawo jama’a daga sassa daban-daban na garin Gombe, ciki har da matasa, dattawa, da sauransu.
Rahoto ya nuna cewa an gudanar da sallar cikin nutsuwa da ladabi, inda aka yi addu’o’in neman gafara da rahama ga Buhari.
Wani mazaunin Gombe da ya halarci jana'izar, Musa Yahaya, ya ce:
“Buhari mutum ne da ya bar tarihi a Najeriya, muna addu’ar Allah ya jikansa. Wannan sallar alama ce ta kauna da mutunta shi.”
Shugabannin duniya za su hallara Daura
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin kasashen duniya za su halarci jana'izar shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Cikin hawaye, Fatima Buhari ta isa Daura inda za a binne gawar mahaifinta
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa shugabannin kasashen Chadi, Guinea Bissau da Gambiya za su halarci jana'izar.
Hakan na zuwa ne bayan manyan baki daga kasashe daban daban da kuma cikin kasa Najeriya da ake sa ran za su hallara jana'izar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

