An Fara Tona Kabarin Muhammadu Buhari a Gidansa na Daura

An Fara Tona Kabarin Muhammadu Buhari a Gidansa na Daura

  • Rahotanni sun ce an zuba jami'an DSS, sojoji, ‘yan sanda da NSCDC a sassan jihar Katsina, yayin da ake jiran karasowar gawar Muhammadu Buhari
  • Shugaban kasa Bola Tinubu zai karɓi gawar Buhari a filin jirgin saman Katsina yayin da aka tabbatar da cewa sun taso daga Landan
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an fara tono kabari a wani sashe na gidansa da ke Daura inda ake sa ran za a rufe tsohon shugaban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – An ƙara matakan tsaro a gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ke Daura a jihar Katsina, yayin da ake sa ran isowar gawarsa daga Landan.

Gawar marigayin, wadda ta riga ta tashi daga birnin London, na kan hanyarta zuwa Najeriya, inda za a sauke ta a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

Kara karanta wannan

Yadda aka dauko gawar Buhari a jirgi daga London zuwa Katsina

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
An fara haka kabarin Buhari Hoto: Zainab Kurawa
Source: UGC

Channels TV ta ruwaito shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da kansa zai karɓi gawar a filin jirgi, tare da rakiyar mataimakinsa, Kashim Shettima, da shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadannan manyan jami’an gwamnatin tarayya suna cikin rakiyar da ke dawo da gawar tsohon shugaban daga Birtaniya.

Jami’an tsaro sun cika gidan Buhari

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Talata, gidan Buhari da ke Daura ya cika da jami’an tsaro, ciki har da jami'an hukumar DSS da sojojin Najeriya.

Haka kuma, 'yan sanda da jami’an tsaron fararen hula (NSCDC) sun mamaye wasu muhimman wurare da ke cikin Daura domin tabbatar da tsaro yayin isowar gawar.

Wata majiya daga gidan marigayin ta tabbatar da cewa an fara tona kabari a wani bangare na gidan domin birne marigayin idan gawarsa ta sauka a gida.

Yadda ake shirin birne Buhari

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta ce an ware wajen da za a birne Buhari, kuma ana shirin zagaye wurin da katanga da zarar an kammala rufe shi.

Kara karanta wannan

'Ya yiwa yan Najeriya iya kokarinsa,' Abin da AbdulSalami ya ce kan Buhari

Muhammadu Buhari, tsohon shugaban Najeriya
Ana jiran gawar Muhammadu Buhari a Daura Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Twitter

A cewar Garba Shehu, mai magana da yawun marigayi shugaban kasa, ana sa ran gawar Buhari za ta iso tsakanin karfe 11.00 na safe zuwa 12.00 na rana a yau Talata.

Sai dai ya bayyana cewa za a bar gwamnatin jihar Katsina ta yanke hukunci kan inda za a gudanar da sallar jana’izar shugaban.

Abin da AbdulSalami ya ce kan Buhari

A baya, mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya bayyana alhinin rasuwar Muhammadu Buhari a birnin Landan.

Tsohon shugaban ya ce jim kadan bayan da aka sallame shi daga asibitin da suke kwance tare da Buhari ne ya samu labarin rasuwarsa, lamarin da ya jefa shi a cikin jimami.

Tsohon shugaban ya yaba da yadda Buhari ya gudanar da rayuwarsa cikin gaskiya da amana, tare da cewa rasuwarsa babban rashi ne ga Najeriya da ma nahiyar Afrika baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng