Sojoji Sun Hana Mabiya Addinin Gargajiya Kusantar Wurin Jana'izar Sarki Musulmi

Sojoji Sun Hana Mabiya Addinin Gargajiya Kusantar Wurin Jana'izar Sarki Musulmi

  • Sojoji sun hana yan addinin gargajiya shiga jana'izar fitaccen basarake da aka gudanar a bisa tsarin Musulunci
  • An birne marigayi Oba Sikiru Adetona, bisa koyarwar Musulunci, inda aka yi masa addu'o’i tare da jagorancin Babban Limamin Ijebu
  • Shugabanni da dama ciki har da Aliko Dangote, Yemi Osinbajo da Gwamna Dapo Abiodun sun yaba da jajircewar marigayin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - An gudanar da sallar jana'izar fitaccen basarake bisa koyarwar Musulunci a Najeriya.

Marigayi Sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona ya rasu a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 da muke ciki.

An gudanar da sallar jana'izar Sarki da ya rasu
Sojoji sun dakile yan addinin gargajiya zuwa jana'izar Sarki. Hoto: Oba Sikiru Adetona.
Source: UGC

An yi sallar jana'izar Sarkin Ijebu

Punch ta ce sojoji sun hana wasu mabiya addinin gargajiya da ake zargin 'yan kungiyar Osugbo ne shiga jana’izar Musulunci ta marigayin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun ce an yi jana'izar marigayi Awujale na Ijebu, Oba Sikiru Adetona bisa koyarwar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

An yi wa Buhari sallar jana'iza a Gombe yayin da ake jiran gawar shi a Daura

Zuwan ‘yan kungiyar ya jawo fargaba, amma mutane suka fara musu ihu, inda sojoji suka mamaye wurin suka fitar da su daga gidan sarauta.

An birne sarkin a gidansa dake Ijebu Ode da misalin karfe 6:00 na yamma, bisa tsarin Musulunci kamar yadda addininsa ya tanada.

Yadda aka kusa samun rigima a jana'izar Sarki

A ranar Litinin ne ‘yan Osugbo suka bayyana domin su ga ko za su iya kwace ikon jana'izar gabanin binne sarkin wanda ya taimaka wajen sauya dokar jihar.

Amma dai sojoji suka hana su shiga ko kawo hargitsi yayin jana’izar sarkin wanda aka ce shi ne ya jagoranci gyaran dokar.

Oba Adetona, wanda ya yi mulki tsawon shekara 65, ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 yana da shekara 91 da haihuwa.

An birne shi kusa da kabarin mahaifinsa a wani makabartar gida da ake kyautata zaton mahaifiyarsa ma can aka binne ta.

Kafin a birne shi, an gudanar da sallar jana’iza karkashin jagorancin Babban Limamin Ijebu, Sheikh Muftaudeen Ayanbadejo.

Gwamna ya fadi alherin da marigayi Sarki ya bari
Gwamna Dapi Abiodun ya halarci jana'izar Sarkin Ijebu. Hoto: Prince Dapo Abiodun.
Source: Facebook

Manyan Najeriya sun halarci jana'izar Sarkin Ijebu

Kara karanta wannan

Shugabannin kasashen duniya 3 za su hallara Daura jana'izar Buhari

Manyan da suka halarci jana’izar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo (SAN), da gwamnoni kamar su Dapo Abiodun da Babajide Sanwo-Olu da Aliko Dangote.

Gwamna Abiodun ya ce:

“Mulkin Oba Adetona ya samu karbuwa saboda basirarsa, sadaukarwarsa da kokarinsa wajen zaman lafiya da ci gaban Ijebu da Najeriya.”

Ya kara da cewa sarkin ya kasance ginshiki, mai gaskiya da rikon amana, wanda ya sadaukar da mulkinsa wajen hidimar al'umma.

Gwamnan ya bayyana cewa za su yi kewar hikima da shawarwarin sarkin musamman lokacin da yake fuskantar kalubale a 2019.

Aliko Dangote ya yabawa sarkin da irin soyayyar da yake nunawa kowa ba tare da la’akari da daga inda mutum ya fito ba.

Ya ce marigayin sarki ya kasance shugaba nagari da ya ba da gudunmawa wajen ci gaban kasa, kuma ya cancanci a yi koyi da shi.

An dauko gawar Buhari domin jana'izarsa

Kun ji cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa an ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari daga London zuwa Daura.

An ce za a gudanar da sallar jana'izarsa da misalin ƙarfe 2:00 na ranar yau Talata 15 ga watan Yulin 2025 da muke ciki.

Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da wasu manyan jami'an gwamnati za su karɓi gawar a Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.