Bola Tinubu Zai Karɓi Gawar Buhari da Kansa a Katsina, Ya Tura Ministoci 25 Daura
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya tafiya Katsina domin karɓar gawar Muhammadu Buhari da kansa a gobe Talata, 15 ga watan Yuli
- Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ne ya sanar da hakan, ya ce ana sa ran isowar gawar da karfe 12:00 na tsakar rana a gobe Talata
- Bayan isowar gawar, an shirya yin faretin girmamawa na sojoji kafin daga bisani a wuce Daura domin yi wa marigayin jana'iza
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Shugaba Bola Tinubu zai tafi Katsina ya tarbi gawar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, kafin a yi jana’izarsa a Daura.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama'a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Litinin.

Source: Twitter
A cewar Muhammed Idris, ana sa ran gawar Buhari wanda ya rasu a wani asibiti da ke Landan ranar Lahadi, zata iso Najeriya da ƙarfe 12:00 na rana gobe Talata, rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu zai tarbi gawar Buhari a Katsina
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, zai karɓi gawar tsohon Shugaba Buhari da kansa a Katsina. Bayan isowar gawar, za a gudanar da faretin girmamawa na soji a filin jirgin sama kafin a wuce zuwa Daura.
“Za a gudanar da sallar jana’iza bayan haka, sannan a binne shi a mahaifarsa da ke Daura,” in ji Idris.
Ya ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yanzu haka yana Landan, inda yake jagorantar tawagar gwamnatin tarayya domin kammala duk wasu takardu da shirye-shiryen dawo da gawar gida Najeriya.
Za a buɗe litattafai a ma'aikatu da hukumomi
Ministan ya bayyana cewa a matsayin wani ɓangare na zaman makoki na ƙasa, Shugaba Tinubu ya umurci a buɗe litattafan ta’aziyya a dukkan Ma’aikatun Tarayya da Hukumomi (MDAs).
Ya ƙara da cewa za a kuma buɗe littafin ta’aziyya na musamman a Cibiyar Taro ta Ƙasa da ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Muhammaed Idris ya kuma bayyana cewa shugabannin ƙasashe da dama na ci gaba da aiko da saƙonnin ta’aziyya, Tribune Nigeria ta rahoto.

Source: Getty Images
Tinubu ya tura ministoci 25 zuwa Katsina
Domin tabbatar da tsari mai inganci, Mohammed Idris ya ce Shugaba Tinubu ya kafa Kwamitin jana'iza karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Kwamitin zai yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Katsina da iyalan marigayi Buhari domin tsara dukkan ayyukan da suka shafi jana’iza Muhammadu Buhari.
Ministan ya ce tuni Tinubu ya umarci mambobi 25 na Majalisar Zartarwa ta Tarayya su tafi Katsina domin halartar jana’iza sannan su zauna a Daura har zuwa ranar Laraba don a yi addu'ar 3 da su.
Daurawa ya roki a yafewa Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya roki ƴan Najeriya su sanya Muhammadu Buhari a addu'o'insu kana su yafe masa kura-kuransa.
Ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan yafewa Buhari laifin da wataƙila ya aikata lokacin da yake shugabancin Najeriya.
Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi ƴan Najeriya su yafewa Marigayi Buhari kura-kuran da wataƙila ya aikata masu.
Asali: Legit.ng

