Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya ba Ministoci 10 Muhimmin Aiki kan Jana'izar Buhari
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwamitin ministoci da manyan jami'an gwamnti domin shirya jana'izar Muhammadu Buhari
- Kwamitin wanda ya ƙunshi ministoci 10, NSA da ƙunsoshin gwamnati zai yi aiki ne ƙarƙashin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume
- Tinubu ya kuma umarci duka ma'aikatu da hukumomin gwamnati su buɗe littafin ta'aziyya domin jajen rasuwar Buhari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da ƙirƙirar Kwamitin Jana'izar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu kafa wannan kwamiti da ya kunshi ministoci 10 domin shiryawa da kuma tsara jana’izar ƙasa ta musamman ga marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, GCFR.

Source: Twitter
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ta wallafa a shafinta na X yau Litinin, 13 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ɗora wa kwamitin, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, CON, zai jagoranta, alhakin tsarawa da gudanar da jana’izar da ta dace da darajar marigayi Buhari.
Ministoci da jiga-jigan kwamitin jana'iza
’Yan kwamitin sun haɗa da:
1. Ministan kuɗi kuma mai Kula da harkokin tattalin arzikin ƙasa, Wale Edun.
2. Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na tattalin arziki, Atiku Bagudu.
3. Ministan tsaro, Badaru Abubakar.
4. Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris.
5. Ministan ayyuka, Dave Umahi.
6. Ministan harkokin cikin gida, Tunji-Ojo
7. Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike
8. Ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmad Ɗangiwa
9. Ƙaramin ministan lafiya.
10. Ministar al’adu da kirƙire-kirkire, Hannatu Musawa.
11. Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron, Malam Nuhu Ribaɗu.
12. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan tsare-tsare da daidaitawa;
13. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa, Kabir Masari.
14. Sufeto Janar na ’Yan Sanda
15. Darakta Janar na Hukumar DSS;
15. Babban Hafsan Hasoshin Tsaro (CDS).
Ofishin babban sakataren sashen harkokin gwamnati (GSO), zai kasance a matsayin sakatariyar kwamitin.

Source: Twitter
Tinubu ya kara ɗaukar matakan karrama Buhari
Domin girmamawa ga Buhari, Shugaba Tinubu ya umarci dukkan Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati (MDAs) su buɗe litattafan ta’aziyya a ƙofofin ofisoshinsu domin bai wa jama’a damar yin jaje.
Bugu da ƙari, za a buɗe babban littafin ta’aziyya ga jakadun ƙasashen waje da sauran jama’a a Ma’aikatar Harkokin Waje da babban ɗakin taron Bola Ahmed Tinubu, Abuja.
Buhari: Darasi 1 da shugabanni za su ɗauka
A wani labarin, kun ji cewa Farouk Aliyu ya bayyana cewa darasi ɗaya da ya kamata shugabanni su ɗauka daga rasuwar Muhammadu Buhari shi ne akwai mutuwa.
Farouk ya ƙara da cewa duk da Buhari na da wasu kurakurai, ya kamata a girmama shi saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasa.
Ya nuna damuwa kan yadda wasu ke sukar Buhari da zagi a kafafen sada zumunta, yana mai cewa a yanzu addu'a yake buƙata da kuma.girmamawa.
Asali: Legit.ng

