'Darasi 1 da Ya Kamata Shugabannin Najeriya Su Ɗauka daga Rasuwar Shugaba Buhari'
- Farouk Aliyu ya bayyana cewa darasi ɗaya da ya kamata shugabanni su ɗauka daga rasuwar Muhammadu Buhari shi ne rayuwa ba ta dawwama
- Abokin siyasar Buhari ya ce duk matsayin da mutum ya taka a rayuwa duk ƙololuwarsa, wata rana mutuwa za ta riske shi
- Farouk ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu ƴan Najeriya ke faɗar baƙaƙen magangantu kan Marigayi Buhari a kafafen sada zumunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Farouk Aliyu, ɗaya daga cikin na kusa da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya buƙaci shugabannin Najeriya su riƙa tuna mutuwa.
Farouk Aliyu ya yi kira ga shugabanni a matakai daban-daban a Najeriya da su ɗauki darasi daga rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Buhari.

Source: Instagram
Abokin siyasar Buhari, wanda ya jima tare da marigayin, ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin Sunrise Daily na Channels tv ranar Litinin.

Kara karanta wannan
Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farouk Aliyu ya fusata da masu zagin Buhari
Farouk ya ƙara da cewa duk da Buhari na da wasu kurakurai, ya kamata a girmama shi saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya.
Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda wasu ƴan Najeriya ke maganganu marasa daɗi kan Buhari a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan bai kamata ba a irin wannan lokacin, rahoton Tribune Nigeria.
Ya jaddada muhimmancin shugabanni su tuna rayuwa ba ta dawwama, yana mai kawo misalan mutuwar wasu shahararrun shugabannin Najeriya kamar su Murtala Muhammed, Ernest Shonekan, Shehu Shagari da Sani Abacha.
Wane darasi shugabanni za su ɗauka?
A cewarsa, duka waɗannan da ma Buhari, wanda ya rasu kwanan nan, tsofaffim shugabanni ne waɗanda a yanzu duk sun koma ga mahaliccinsi.
“Mu da muke a matsayin shugabanni ya kamata mu lura cewa abubuwa ba za su dawwama ba. Mutuwa dole ce, rayuwar nan da muke yi tana da iyaka.
“Saboda haka, duk matsayin da mutum ya samu kansa a kai a wannan rayuwar, ko shugaban ƙasa ne, ko gwamna, ko wane irin matsayi ne, mutuwa za ta riske shi kuma dole ya tafi.
- In ji Farouk Aliyu.

Source: Instagram
Farouk Aliyu ya nemi a girmama Buhari
Ya nuna damuwa kan yadda wasu ke sukar Buhari da zagi a kafafen sada zumunta, yana mai cewa a yanzu addu'a yake buƙata da kuma girmamawa.
“Idan ka duba kafafen sada zumunta, za ka ga cewa mutane da yawa (’yan Najeriya) na zagin marigayi tsohon shugaban ƙasa (Buhari). Wannan abin takaici ne," in ji shi.
Bola Tinubu ya ba da hutu saboda rasuwar Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ba da hutun gobe Talata, 15 ga watan Yuli saboda rasuwar Muhammadu Buhari.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, bayan amincewar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tunji-Ojo.ya ƙara da cewa an ayyana hutun ne domin bai wa ƴan Najeriya dama su yi tunani a kan gudunmawar da marigayi tsohon shugaban ƙasar ya bayar a rayuwarsa.
Asali: Legit.ng
