Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu saboda Rasuwar Buhari
- Gwamnatin tarayya ta ba da hutu sakamakon rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu a Landan
- An ayyana ranar Talata a matsayin lokacin hutu don karrama Muhammadu Buhari wanda ya yi bankwana da duniya a ranar Lahadi
- Gwamnatin tarayya ta kuma miƙa saƙon ta'aziyyarta ga iyalan Buhari, gwamnatin jihar Katsina da kuma ƴan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu domin girmama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar hutu don girmama Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma'aikatar harkokin cikin gida Magdalene Ajani ta fitar a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta ba da hutu saboda rasuwar Buhari
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, bayan amincewar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Wannan sanarwar na daga cikin jerin matakan da ake ɗauka a lokacin makoki na kwana bakwai da shugaban ƙasa ya ayyana domin karrama rayuwar marigayi Buhari.
Buhari ya rasu yana da shekaru 82 a wani asibiti da ke birnin Landan, kuma tsohon mai ba shi shawara ta musamman, Garba Shehu, ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar da yamma ranar Lahadi.
A cikin sanarwar da Magdalene Ajani ta fitar, Tunji-Ojo ya bayyana Buhari a matsayin shugaba wanda ya bauta wa Najeriya cike da sadaukarwa da gaskiya.
Meyasa gwamnati ta ba da hutu?
Ya ƙara da cewa an ayyana hutun ne domin bai wa ƴan Najeriya dama su yi tunani a kan gudunmawar marigayi shugaban ƙasan wajen tafiyar dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa.

Source: Twitter
“A ci gaba da makoki na kwana bakwai da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ayyana, gwamnatin tarayya ta bayyana Talata, 15 ga watan Yuli, 2025, a matsayin ranar hutu na ƙasa domin girmama marigayi tsohon shugaban tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari."

Kara karanta wannan
Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2
“Wannan hutu yana nuna girmamawa ga hidimar da marigayi shugaban ya yi wa ƙasa, gudunmawarsa wajen tafiyar da dimokuraɗiyya da kuma gado mai ɗorewa da ya bari a harkar mulki da ci gaban ƙasa."
"Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Najeriya hidima da gaskiya, sadaukarwa, da cikakken kishin ƙasa wajen tabbatar da haɗin kai da cigaban ƙasarmu mai albarka."
"Wannan rana ta hutu dama ce ga ƴan Najeriya su yi tunani a kan rayuwarsa, shugabancinsa, da kuma ƙimomin da ya tsaya kai da fata a rayuwarsa."
- Dr. Olabunmi Tunji-Ojo
Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayi shugaban ƙasan, al’ummar jihar Katsina, da duk ƴan Najeriya, tare da addu’ar Allah ya jikan ruhinsa da rahama.
Yadda Buhari ya tsira daga yunƙurin kisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa a shekarar 2014, an taɓa yunƙurin hallaka tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Buhari dai ya tsallake rijiya da baya bayan da aka tayar da bama-bamai a kusa da motarsa a jihar Kaduna.
A lokacin dai, Buhari ya tsira ne sakamakon yana cikin wata mota da harsashi bai fasawa wacce Rabiu Musa Kwankwaso ya ba shi.
Asali: Legit.ng
