Mufti Menk Ya Yi Ta'aziyyar Buhari, Ya Tuna Ɗabi'arsa game da Sallah

Mufti Menk Ya Yi Ta'aziyyar Buhari, Ya Tuna Ɗabi'arsa game da Sallah

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci, Mufti Menk, ya yi jimami kan rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • Mufti Menk ya roƙi Allah SWT Ya yi wa Buhari rahama, Ya ba iyalansa hakuri da ƙarfin jure wannan babban rashi
  • Haka kuma ya bayyana wasu daga halayen kirkin da ya ce tsohon shugaban yana da su, daga ciki har da riko da Sallah

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Mufti Menk, ya bayyana ta’aziyyarsa kan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban ya rasu ranar Lahadi a birnin Landan, inda Mufti Menk ya shiga cikin jerin malamai da ‘yan Najeriya da ke ta’aziyya kan rasuwar Buhari.

Mufti Menk da Muhammadu Buhari
Mufti Menk ya yiwa Najeriya ta'aziyya Hoto: @muftimenk
Source: Twitter

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Sheikh Mufti Menk ya bayyana Buhari, a matsayin mai ibada da amana.

Kara karanta wannan

Sun kwanta dama: Buhari, Dantata da wasu manyan ƴan Najeriya da suka rasu a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu haka ana ta shirye-shiryen yadda za a dawo da gawar tsohon shugaban zuwa Daura da ke jihar Katsina domin yi masa sutura.

Mufti Menk ya yaba halayen Buhari

Sheikh Mufti Menk ya bayyana kyakkyawan halin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajen riko da addini, gaskiya da rikon amana.

Ya ce:

“Rasuwar Muhammadu Buhari ya taba ni sosai! Mutum ne nagari, wanda bai taba bari sallah ta wuce shi ba."
"Yana da da’a sosai kuma ya yi wa mutanensa hidima gwargwadon iko.”

Addu’oin Mufti Menk ga Buhari da iyalansa

Mufti Menk ya yi addu’ar Allah Subhanahu wa Ta’ala da Ya yi wa Buhari rahama, tare da roƙon Allah Ya ba iyalansa da abokansa hakuri da ƙarfin halin jure wannan babban rashi.

Ya ce:

“Ya Allah Mai girma, Ka gafarta masa kuma Ka ba shi Aljannah. Ameen. Ka kuma sauwakawa iyalansa, abokansa da dukkanin 'yan Najeriya.”

Yan Najeriya sun yi ta’aziyyar Buhari

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Buhari ya tsira bayan yunkurin kashe shi a 2014

'Yan Najeriya da dama sun bi sakon Mufti Menk a shafin inda suka yi ta'aziyya da addu'o'i ga tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Mufti Menk ya yiwa Buhari addu'a Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Getty Images

@0xjulia_ ta ce:

“Shugaban kasa ne na gari a zamaninsa, ya kyautata wa jama'a a lokacinsa.”

@Isabelloisa1:

“Allah Ya gafarta masa. Ameen.”

@folashade_aduke ta ce:

'Muna alhinin rasuwar tsohon shugaban kasa, wanda ya yi aikin hada kan kasar mu wuri guda."

@hassan__magaji ya ce:

"Mun gode Sheikh. Allah Ya Yi masa rahama. Duk inda aka ambaci sunan shi, ana kiransa mai gaskiya."

@menszn ya wallafa cewa:

"Mutumin kirki ne, ya yiwa Najeriya hidima."

Ganduje ya fadi nagartar Buhari

A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana alhini kan rasuwar Muhammadu Buhari.

Ganduje ya bayyana marigayi Buhari a matsayin gwarzon ɗan ƙasa da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa Najeriya kuma bai saurarawa yaƙi da rashawa ba.

Ya ƙara da cewa Buhari ya rayu da gaskiya da tarbiyya tun daga lokacin da yake a rundunar soji har zuwa lokacin da ya zama shugaban ƙasa na farar hula sau biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng