Tuna Baya: Yadda Buhari Ya Tsira bayan Yunkurin Kashe Shi a 2014
- Ana ci gaba da alhini tare da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasan Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin Landan
- Marigayi Buhari ya taɓa tsallake rijiya da baya a shekarar 2014, bayan da aka yi yunƙurin kashe shi a wani harin bam
- A lokacin harin dai, mutane da dama sun rasu amma Allah Ya sanya Buhari ya tsira da ransa ba tare da samun rauni ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taɓa tsallake rijiya da baya yayin da aka yi yunƙurin kashe shi.
Tsohon shugaban ƙasan na Najeriya dai ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce a watan Yuli na shekarar 2014, Buhari ya tsira daga harin bama-bamai da Boko Haram suka kai a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kai wa Buhari harin bam a 2014
Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa aƙalla mutane 82 ne suka mutu a yayin harin.
Yayin da Buhari ya tsira ba tare da rauni ba a fashewar bama-baman da ta faru a yankin kasuwar Kawo da ke cunkoson mutane a birnin Kaduna, wasu jami’an tsaronsa guda uku sun ji rauni kuma aka garzaya da su asibiti.
A lokacin harin, wani hadimin shugaban ƙasa ya bayyana cewa wanda ya kai harin ya zo ne cikin mota ƙirar Toyota Sienna, ya afka cikin jerin gwanon motocin Buhari, sannan ya tarwatsa bama-baman da ke cikin motar.
Duk da cewa Buhari ya tsira daga harin, motarsa ƙirar Toyota Land Cruiser da wata motar da ke biye da ita sun lalace ƙwarai da gaske.
Yadda Buhari ya tsira a harin bam
A cikin wani fim mai taken ‘Essential Muhammadu Buhari’, tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa wata mota da Sanata Rabiu Kwankwaso ya ba shi ce ta taimaka masa wajen tsira daga harin bama-baman.

Kara karanta wannan
Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2

Source: UGC
"Ina ganin Kwankwaso ya nuna kyautatawa. Ya ba ni wata motar Land Rover da harsasahi bai fasawa. Ya ce na riƙa amfani da ita domin yana ganin takarar da nake ciki tana da haɗari, kuma akwai yiwuwar wasu za su so su kashe ni."
"Lokacin da nake kan hanyar zuwa Kano daga Kaduna cikin wannan motar, sai wata mota ta so ta shiga gabanmu, amma ƴan sandan da ke rakiya suka hana su. Sannan suka tarwatsa bama-baman."
"Da na duba waje, sai na ga sassan jikin mutane. Babu wanda ke cikin motarmu da ya ji rauni. Amma sai na ga jini a jikina, saboda yawan mutanen da suka mutu a wajen motar ta dalilin fashewar bama-baman."
- Muhammadu Buhari
Za a birne Muhammadu Buhari a Daura
A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana inda za a yi jana'izar Muhammadu Buhari.
Gwamna Radda ya bayyana cewa za a yi jana'izar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ne a mahaifarsa ta Daura.
Sanarwar hakan dai ta biyo bayan rasuwar da tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ya yi ne a birnin Landan.
Asali: Legit.ng

