Tuna Baya: Kalamai Masu Ratsa Zuciya da Buhari Ya Faɗa kan Ciwon da ke Damunsa

Tuna Baya: Kalamai Masu Ratsa Zuciya da Buhari Ya Faɗa kan Ciwon da ke Damunsa

  • Rahotanni sun nuna cewa ana ta shirye-shiryen jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Daura gobe Talata, 15 ga watan Yuli 2025
  • Buhari ya jima yana fama da jinya tun lokacin yana kan mulki, inda ya rika zuwa birnin Landan da ke ƙasar Burtaniya domin duba lafiyarsa
  • Kalaman da Buhari ya yi bayan ya dawo daga jinyar makonnni bakwai a shekarar 2017, sun nuna irin halin da shugaban ƙasar ke ciki tun a wancan lokaci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da ake shirye-shiryen jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Daura, ana ta tunawa da wasu daga cikin kalaman da ya yi a baya.

Muhammadu Buhari ya rasu ne da yammacin jiya Lahadi a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Ingila bayan ya sha fama jinya.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Buhari ya tsira bayan yunkurin kashe shi a 2014

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari ya shafe makonni 7 yana jinya a 2017 Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

The Nation ta tattaro cewa Buhari ya sha fama da rashin lafiya tun a zangon mulkinsa na farko watau daga 2015 zuwa 2019.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da ya dawo Najeriya a watan Maris, 2017, bayan shafe tsawon lokaci a Landan, Shugaba Buhari ya bayyana halin da ya shiga na rashin lafiya.

Buhari ya faɗi yadda yake ji a 2017

A wancan lokaci, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai taɓa jin rashin lafiya da ta wahalar da shi ba kamar yadda ya ji a ‘yan makonnin da ya shafe a gadon asibiti.

Ya faɗi hakan ne a lokacin da yake jawabi ga manyan baki a babban birnin tarayya Abuja, bayan dawowa daga hutun jinya na makonni bakwai da ya yi a Birtaniya.

Rashin lafiyar tasa a wannan lokaci ta haifar da ce-ce-ku-ce da damuwa a Najeriya, inda mutane suka riƙa hasashe kan lafiyar shugaban ƙasa.

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya ci gaba da jagoranci yayin da Buhari ke jinya, kuma mai magana da yawunsa ya ce zai dawo bakin aiki da ƙarfi.

Kara karanta wannan

'Mun yi babban rashi,' Ganduje ya mika ta'aziyya ga 'yan Najeriya kan rasuwar Buhari

Wace cuta ke damun Shugaba Buhari?

A lokacin da ya dawo a watan Maris, 2017, Shugaba Buhari mai shekara 74 ya sauka a sansanin sojojin sama da ke birnin Kaduna daga London da safiyar Juma’a.

Duk da ya bayyana yadda yake ji, bai fayyace irin cutar da ke damunsa ba a wancan lokacin.

Sai dai ya kwantar da hankulan ƴan Najeriya da cewa ya samu sauƙi sosai amma zai ci gaba da zuwa duba lafiyarsa akai akai.

A ƙarshen jawabin da ya ɗauki kusan mintuna tara, Buhari ya ce yana sane ya dawo a karshen mako "domin mataimakin shugaban ƙasa ya ci gaba da aiki, ni kuma in ci gaba da hutawa."

Muhammadu Buhari ya sha fama da jinya.
Muhammadu Buhari ya ba ƴan Najeriya shawara kan shan magani ba tare da zuwa wurin likita ba Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Shugaba Buhari yana cikin nishadi a lokacin jawabin, inda aka ga yana dariya ga manyan jami’ai da ‘yan jarida.

A jawabin, ya yi magana kan muhimmancin fasaha da ilimi har ma ya ja kunnen ‘yan Najeriya da kada su riƙa shan magani da kansu ba tare da shawarar likita ba.

Kara karanta wannan

Bayan rasuwarsa, an ji yawan kadarorin Buhari da tsabar kuɗi da ya ajiye a banki

Ganduje ya yi alhinin rasuwar Buhari

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi ta'aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari.

Tsohon gwamnan na Kano, Ganduje ya bayyana marigayi Buhari a matsayin gwarzon ɗan ƙasa, wanda ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen kawo ci gaba a Najeriya.

Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Buhari, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, yana mai miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262