'Mun Yi Babban Rashi,' Ganduje Ya Mika Ta'aziyya ga 'Yan Najeriya kan Rasuwar Buhari

'Mun Yi Babban Rashi,' Ganduje Ya Mika Ta'aziyya ga 'Yan Najeriya kan Rasuwar Buhari

  • Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana alhini kan rasuwar Muhammadu Buhari
  • Ya bayyana tsohon shugaban da kishin Najeriya tun daga zamaninsa a soja har zuwa lokacin mulkinsa na dimokuraɗiyya
  • Ganduje ya ce Najeriya gaba ɗaya ta yi babban rashi, ba iyalan Buhari kaɗai ba, yana kuma addu’ar Allah Ya gafarta masa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana alhini da kaduwa bisa rasuwar Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasar ya rasu ne a birnin Landan, Burtaniya a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 bayan ya sha fama da jinya.

Abdullahi Umar Ganduje da Muhammadu Buhari
Ganduje ya fadi yadda Buhari ya rayu Hoto: Gandujiyya Online
Source: Facebook

A sakon da Ganduje Online ta wallafa a shafin Facebook, tsohon gwamnan ya bayyana alhininsa bisa abin da ya kira babban rashi ga dukkanin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 su haɗa baki, sun ba da hutun kwana 1 saboda rasuwar Buhari

Ganduje ya yi ta’aziyyar Buhari

Blueprint ta wallafa cewa ta cikin wata sanarwa da Mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya bayyana marigayi Buhari a matsayin gwarzon ɗan ƙasa.

A cewarsa:

“Rasuwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari babban rashi ne, ba wai kawai ga iyalinsa da al’ummar jihar Katsina ba, har da ƙasar Najeriya gaba ɗaya.”
“Buhari mutum ne da ya ke da gaskiya, tarbiyya da sadaukarwa. Tun daga lokacin da yake soja har zuwa lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban ƙasa, ya kasance mai kishin ƙasa da jajircewa ga ci gaba da haɗin kan Najeriya.”

Ganduje ya yiwa Buhari addu’a

Tsohon gwamnan Jihar Kano ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, gwamnatin Jihar Katsina da daukacin al’ummar Najeriya bisa rashin Buhari.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Ganduje ya yi ta'aziyyar tsohon shugaban Najeriya Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Getty Images

Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Buhari, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

A cikin sanarwar, Ganduje ya ce:

Kara karanta wannan

Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2

“Za a ci gaba da tunawa da Buhari kan yadda ya yaƙi cin hanci da rashawa, yadda ya bunkasa harkar noma da kuma yadda ya jajirce wajen samar da tsaro a ƙasa.”

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da girmama Buhari ta hanyar riko da ƙa’idodin kishin ƙasa, gaskiya da sadaukarwa da marigayin ya rayu a kansu.

Ganduje ya kara da nusar da jama'a a kan su ci gaba da yiwa tsohon shugaban addu'a a lokacin da ake ci gaba da alhinin rasuwar Muhammadu Buhari.

Shawarwarin Buhari lokacin yana raye

A wani labarin, mun wallafa cewa an fara tuna wasu daga cikin shawarwarin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ga 'yan Najeriya a rayuwarsa.

Daya daga cikin abubuwan da ake yawan tunawa da Buhari da su shi ne yadda ya rika jan hankalin ‘yan Najeriya da su zama masu gaskiya da rikon amana.

Tsohon shugaban, ya bayyana dukkanin abubuwan da ke duniya a matsayin abin da bai kamata mutum ya yi riko da su ba, inda ya ce gaskiya ce abin riko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng