Ana Jimamin Buhari, Babban Malamin Musulunci, Abdullahi 'Yankaba Ya Rasu a Kano

Ana Jimamin Buhari, Babban Malamin Musulunci, Abdullahi 'Yankaba Ya Rasu a Kano

  • Shahararren malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Dr Abdullahi Yankaba, ya rasu a safiyar yau Litinin
  • Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 1:30 na rana a cibiyar Islahul Ummah da ke layin Umar Adamu, Yankaba, Kano
  • Masu da’awa da almajirai sun bayyana alhinin su tare da addu’a ga Allah ya jikan marigayin, ya sanya shi a Aljannar Firdausi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Daya daga cikin fitattun malamai a jihar Kano, Sheikh Dr Abdullahi Yankaba, ya rasu a yau Litinin, kamar yadda wasu daga cikin mazauna unguwar suka tabbatar.

Rasuwar marigayin ta girgiza al’ummar musulmi a Kano da wajen ta, musamman dalibansa da suka kwashe shekaru suna cin moriyar karatunsa.

Sheikh Abdullahi Yankaba da ya rasu a Kano
Sheikh Abdullahi Yankaba da ya rasu a Kano. Hoto: Yasir Ramadan Gwale
Source: Facebook

Babban malamin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Muhammad bin Usman ya tabbatar da rasuwar Dr Yankaba a wani sako a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An sake yin babban rashi: Bayan rasuwar Buhari, mai martaba sarkin Ijebu ya mutu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta wallafa cewa za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 1:30 na rana a cibiyar Islahul Ummah da ke layin Umar Adamu, a Yankaba kusa da Dakata, a ƙaramar hukumar Nassarawa.

Sheikh Muhammad Bin Usman ya yi ta'aziyya

Shugaban masallacin Sahaba, Sheikh Muhammad Bin Usman Kano, ya fitar da sakon ta’aziyya a madadin masallacin Sahaba.

A cikin sakon, Sheikh Bin Usman ya ce:

“Cikin alhini da sallamawa ga ƙaddarar Allah muke sanar da rasuwar babban malaminmu Sheikh Dr Abdullahi Yankaba.
"Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokan aikinsa, almajiransa"

Rahotanni sun bayyana cewa Sheikh Muhammad Bin Uthman Kano ya kasance babban abokin marigayin.

Sheikh Muhammad Bin Usman Kano
Sheikh Muhammad Bin Usman Kano. Hoto: Masjidul Sahaba
Source: Facebook

Ya ƙara da addu’ar Allah ya gafarta masa, ya sanya kabarinsa ya zamo wajen samun rahama, ya kuma haɗa su gaba ɗaya a Aljanna.

Jama’a sun nuna alhini a kofar gidansa

Wani mazaunin unguwar Yankaba, Musa Adamu Musa, ya shaida wa Legit Hausa cewa ya ga jama’a da dama sun taru a kofar gidan malamin tun da safiyar yau.

Kara karanta wannan

Atiku, Ganduje, Saraki Barau sun taru a auren ɗan tsohon shugaban ƙasa a Abuja

Musa ya ce:

“Da na fara ganinsu, na dauka sun zo jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Buhari ne, sai daga baya aka shaida min cewa Allah ya yi wa malam rasuwa,”

Ya ce marigayin ya kasance mutum mai tsantsar dattaku da tausayi, wanda ke da kyakkyawar hulɗa da kowa a unguwar.

Ana jimamin rasuwar Sheikh Yankaba

Tun bayan mutuwar Sheikh Dr Abdullahi Yankaba, kafafen sada zumunta suka cika da sakonnin ta’aziyya daga mutane daban-daban, ciki har da almajiransa, abokan da’awa da sauran malamai.

Masu amfani da dandalin Facebook da X sun bayyana rashin marigayin a matsayin babban gibi ga ilimin addini da da’awa a jihar Kano da ma ƙasar baki ɗaya.

Ana jimamin rasuwar Buhari a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya.

Wasu mazauna Daura da ke kusa da gidan Muhammadu Buhari sun bayyana cewa sun shiga damuwa kan rasuwar shi.

Haka zalika wasu da ke kusa da gidan Muhammadu Buhari na jihar Kaduna sun yi jimami da fatan Allah ya gafarta masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng