IBB Ya Tura Sakon Jaje ga Aisha Buhari, Ya Fadi Alakarsa da Mijinta da Ya Rasu
- Tsohon shugaban soja, Janar Ibrahim Babangida, ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin ɗan kishin ƙasa mai gaskiya da jajircewa
- IBB ya ce sun fara haɗuwa ne tun 1962 a makarantar horas da sojoji a Kaduna, kuma sun rike juna a matsayin 'yan uwa duk da bambancin ra'ayi
- Tsohon shugaban kasar ya ce mutuwar Buhari ba kawai mutuwar tsohon shugaban ƙasa ba ce, sai dai rashi ne ga Najeriya baki ɗaya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger – Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana alhini da kaduwa bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Marigayi Muhammadu Buhari ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 a wani asibiti a London.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, IBB ya ce ya samu labarin mutuwar Buhari cikin tashin hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari na da kishin kasa inji IBB
Janar Babangida ya yi magana yana mai bayyana Buhari a matsayin mutum mai kishin kasa, da tsantsar gaskiya da rikon amana.
IBB ya ce tun daga shekarar 1962 da suka fara haduwa a makarantar horar da sojoji ta Kaduna, Buhari ya bayyana a matsayin mutum mai nutsuwa, tsari da cikakken kishin ƙasa.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa IBB ya ce:
“Tun daga wancan lokaci Buhari ya riga ya yi fice, mai hankali ne, mai jajircewa, mai tsari ne, mai tawali’u, kuma mai cikakken kishin kasa.”
Buhari da IBB sun rike juna kamar 'yan uwa
Babangida ya ce dangantakarsa da Buhari ta kai matakin da suka daina ganin kansu a matsayin abokan aiki kawai, har suka dinga mu'amala da juna a matsayin 'yan uwa.
Ya kara da cewa ko da yake sukan samu sabani a wasu lamura, hakan bai taɓa hana shi ganin Buhari a matsayin jajirtaccen ɗan ƙasa ba.
Buhari ya tsaya tsayin daka kan gaskiya
IBB ya bayyana cewa Buhari ya nuna gaskiya da rikon amana har zuwa ƙarshen rayuwarsa, yana mai cewa a matsayinsa na shugaban ƙasa da kuma tsohon shugaban soja.
“A kowane matsayi da ya rike, Buhari ya kasance mutum mai kishin ƙasa. Ko da kuwa wasu basu fahimce shi ba, amma ya tsaya a kan akidarsa,”
Inji Babangida
Ya ce Buhari ya kasance mutum mai tsoron Allah, wanda bai taɓa barin girman matsayinsa ya rinjayi halayensa ba.
Sakon Janar IBB ga Aisha Buhari
Janar Babangida ya mika ta’aziyya ga matar Buhari, Aisha Buhari, da ’ya’yansa da jikokinsa, da kuma daukacin al’ummar Najeriya.

Source: Twitter
“Allah ya gafarta masa, ya karɓi ayyukansa na alheri, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus,”
Inji shi.
Tarihin shigar Buhari aikin soja
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fadi dalilin shigar shi aikin soja kafin rasuwar shi.
Marigayin ya bayyana haka ne kwanaki kafin rasuwar shi a wata hira da ya yi tare da tsohon ministan shi, Sheikh Isa Ali Pantami.
A hirar, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya gudu daga gida ne a 1962 ya shiga aikin soja saboda za a masa aure.
Asali: Legit.ng


