Rasuwar Buhari: Gwamna Radda Ya Ayyana Ranar Hutu a Katsina

Rasuwar Buhari: Gwamna Radda Ya Ayyana Ranar Hutu a Katsina

  • Ana ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin Landan na ƙasar Birtaniya
  • Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya ayyana ranar hutu saboda rasuwar Buhari wanda yake ɗan asalin garin Daura ne
  • Za a gudanar da jana'izar tsohon shugaban ƙasan ne a garin Daura a ranar Litinin, 14 ga watan Yulin 2025

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ayyana ranar hutu saboda rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Gwamna Dikko Radda ya bayyana ranar Litinin, 14 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar da babu aiki a jihar Katsina.

Gwamna Radda ya ba da hutu a Katsina
Gwamna Radda ya ba da hutu saboda rasuwar Buhari Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X da daren ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

IBB ya tura sakon jaje ga Aisha Buhari, ya fadi alakarsa da mijinta da ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Buhari ya rasu

Tun da farko Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.

Tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ya koma ga mahaliccinsa ne a wani asibiti da ba a bayyana ba a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Buhari dai ya kwashe kwanaki yana jinyar rashin lafiya wacce ba a bayyana kowace iri ba ce kafin rasuwarsa.

A kwanakin baya an yaɗa jita-jitar cewa tsohon shugaban ƙasan ya yi bankwana da duniya, amma daga bisani an fito an ƙaryata hakan.

Ana sa ran dai za a gudanar da jana'izar tsohon shugaban ƙasan ne a mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina.

Tuni dai tsofaffin shugabanni da manyan masu faɗa a ji suka aike da saƙon ta'aziyyarsu kam rasuwar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya.

Rasuwar tsohon shugaban ƙasan dai ta girgiza al'ummar Najeriya waɗanda suka shiga jimami da alhini.

Kara karanta wannan

Buhari: An sanar da ranar jana'izar tsohon shugaban kasa bayan rasuwa a Landan

Gwamna Radda ya ba da hutu a Katsina

A cikin sanarwar da gwamnan na Katsina ya fitar, ya bayyana cewa ya ba da hutun ne domin tunawa da tsohon shugaban ƙasan na Najeriya.

Gwamna Radda ya ba da hutu a Katsina
Gwamna Dikko Radda ya ayyana ranar hutu a Katsina kan rasuwar Buhari Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Radda ya yi addu'ar Allah Ya jiƙan Muhammadu Buhari Ya kuma gafarta masa tare da sanya shi a gidan Aljannah.

"Domin tunawa da rasuwar tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari, na ayyana Litinin, 14 ga watan Yuli, 2025 a matsayin ranar hutun aiki a cikin jihar."
"Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, kuma Ya saka masa da gidan Aljannah saboda ayyukansa na alheri."

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Lokacin da za a yi jana'izar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana ranar da za a yi jana'izar tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin Landan.

Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa za a yi jana'izar marigayin ne a ranar Litinin, 14 ga watan Yulin 2025.

Ana sa ran shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran tsofaffin shugabannin Najeriya za su halarci jana'izar Buhari wacce za a gudanar a garin Daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng