Buhari: An Sanar da Ranar Jana'izar Tsohon Shugaban Kasa bayan Rasuwa a Landan
- Za a dawo da gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa gida Najeriya a ranar Litinin daga birnin Landan
- Ana sa ran Shugaban ƙasa Bola Tinubu da sauran tsofaffin shugabanni za su halarci jana'izar wacce za a yi a mahaifarsa da ke Daura
- Tun da farko dai mai girma Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima da ya je Landan domin yi wa gawar Buhari rakiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ana sa ran shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da wasu daga cikin tsofaffin shugabannin Najeriya za su halarci jana'izar Muhammadu Buhari.
Shugaba Tinubu da sauran shugabannin za su hallara Daura a yau (Litinin) domin jana’izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Source: Twitter
Za a kawo gawar Buhari Najeirya
Wasu jami’an fadar shugaban ƙasa da suka tattauna da jaridar The Punch da yammacin Lahadi sun tabbatar da cewa za a kawo gawar tsohon shugaban ƙasar zuwa gida Najeriya da sassafe a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kawo gawar ne ta tsohon shugaban ƙasan domin kai ta garinsa na Daura, jihar Katsina, don yi masa jana'iza.
A bisa umarnin Shugaba Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne zai rako gawar Buhari daga birnin Landan inda ya rasu a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a agogon Najeriya.
Yaushe za a yi jana'izar Buhari
Ɗaya daga cikin jami’an ya bayyana cewa:
"Jana'izar gobe ne (Litinin). Za a kawo gawarsa cikin dare. Za su wuce kai tsaye zuwa Daura. Don haka za a binne shi gobe. Kamar yadda kuka sani, tsarin Musulunci baya ɗaukar lokaci."
Wata majiya ta ƙara da cewa:
"Da zarar an kawo gawar, muna da tabbacin cewa shugaban ƙasa zai je wajen. Bayan sun isa Daura, zai iya bin su can."
Game da yiwuwar zuwan wasu shugabannin ƙasashen Afirka domin yin gaisuwar ta'aziyyar rasuwar, wani jami’i na uku ya bayyana cewa:
"Eh, za su kasance kusan shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka. Amma ba mu san wa da wa ba har sai sun fara bayyanawa a ranar Litinin."
"Za a kawo gawar da sassafe gobe kuma za a binne shi. Daga nan ne za mu fara karɓar baki daga shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka. Akwai yiwuwar wasu su zo."
"Idan sun zo, za su zauna a otal-otal ɗinsu har sai lokacin da aka tsara su gana da shugaban ƙasa a gobe (Litinin)."
"Kamar yadda kuka sani, Shugaba Tinubu ya dawo ne da safiyar yau (Lahadi), kuma har yanzu yana hutawa."

Source: Facebook
Tun da farko, Shugaba Tinubu ya sanar da rasuwar magabacinsa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu bayan fama da wata doguwar rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Matakan da Tinubu ya ɗauka bayan rasuwar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami a Najeriya bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauki wasu jerin matakai bayan samun labarin rasuwar Buhari.
Daga cikin matakan akwai tura Kashim Shettima domin yi wa gawar Buhari rakiya daga birnin Landan na ƙasa Birtaniya.
Asali: Legit.ng

