Garba Shehu: Yadda ake Shirin Dawo da Gawar Muhammadu Buhari zuwa Daura
- Shirye-shiryen jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba a Najeriya, inda ake shirin birne shi a Daura
- Garba Shehu ya ce ana shirya gawar a asibiti yayin da ake dakon Kashim Shettima domin dawo da ita Buhari zuwa gida
- Tsohon hadimin ya roƙi ‘yan Najeriya da ke jin Buhari ya bata musu rai da su yafe masa, yana mai cewa mutuwa tana kan kowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Yanzu haka ana ci gaba da shirye-shiryen jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya.
Hadiman tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato Garba Shehu da Bashir Ahmad, sun tabbatar da rasuwarsa da yammacin ranar Lahadi.

Source: UGC
A wata hira da Garba Shehu ya yi da Freedom Radio, wacce aka wallafa a shafin na Facebook, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa don dawo da gawar tsohon shugaban kasa zuwa gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana shirin dawo da gawar Buhari Najeriya
Garba Shehu ya bayyana cewa yanzu haka ana dakon isar Kashim Shettima zuwa asibitin da gawar Muhammadu Buhari ta ke inda ake shiryata domin dauko ta zuwa Najeriya.
Ya kara da bayyana cewa:
“Yanzu ana shirya gawar daga asibiti, sannan sai a saurari wakilcin da shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya tura — Kashim Shettima — domin ya je ya taho da gawar, sannan a san lokacin da za su taso.
Garba Shehu ya tabbatar da cewa za a birne tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari a garinsa na haihuwa, Daura, da ke jihar Katsina.
An roƙa wa Buhari afuwa daga 'yan Najeriya
Garba Shehu ya bayyana alhini kan rasuwar ubangidansa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cewar Garba Shehu, yana taya ‘yan Najeriya jimamin wannan babban rashi da ya auku a birnin Landan, inda Buhari ya rasu.

Source: Facebook
Ya kuma roƙi ‘yan Najeriya da ke ganin cewa Buhari ya taɓa bata masu rai da su yafe masa, inda ya ce mutuwa tana kan kowa.
“Ina fatan duk wanda yake jin ya bata masa, Allah Ya ba shi ikon ya yafe wa Muhammadu Buhari."
An sanar da inda za a birne Buhari
A baya, mun wallafa cewa da yammacin Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025, aka samu tabbacin rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a wani asibiti da ke Landan.
Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwar, inda suka ce ya rasu ne yana karɓar kulawar likitoci a birnin Landan na ƙasar Ingila bayan ya shafe dogon lokaci yana jinya.
A wata hira da aka da shi, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya tabbatar da cewa za a yi jana'izar Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina idan sun iso Najeriya.
..ubangidansa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cewar Garba Shehu, yana taya ‘yan Najeriya jimamin wannan babban rashi da ya auku a birnin Landan, inda Buhari ya rasu.
a taɓa bata masu rai da su yafe masa.
Asali: Legit.ng

