Mutuwar Buhari: Yadda aka Shiga Rudani a Daura da Kaduna

Mutuwar Buhari: Yadda aka Shiga Rudani a Daura da Kaduna

  • Mutuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta jefa Daura cikin jimami da kaɗuwa, inda jama'a ke bayyana alhini sosai
  • Maƙwabtan Buhari a Kaduna da mutanen Daura sun bayyana bakin cikin su, suna addu'a Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da Aljannah
  • Masarautar Daura ta tabbatar da rasuwarsa, sai dai har yanzu sarkin karamar hukumar bai fito bainar jama’a ya yi jawabi kan mutuwar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Jimami da kaɗuwa ne suka mamaye garin Daura, mahaifar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bayan tabbatar da rasuwarsa a birnin London a jiya Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.

Jama’a da dama sun nuna damuwa da jimami, inda aka ga tarin mutane sun taru suna tattaunawa da juna, suna kuma mika ta’aziyya.

Kara karanta wannan

Gwamna Radɗa ya sanar da wurin da za a yi jana'izar Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari a gonar shi ta Daura a 2017
Shugaba Buhari a gonar shi ta Daura a 2017. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wasu mazauna garin sun ce mutuwar Buhari babban gibi ne ga yankinsu da kuma ƙasar baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a na kuka da roƙon rahama ga Buhari

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen Daura suna addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi.

Daya daga cikin mazauna Daura, Umar Kamal, ya ce:

“Muna roƙon Allah ya gafarta masa, ya saka masa da Aljannatul Firdausi.”

Wani dattijo a Daura, Muhammad Salisu ya ce ko da yake mutane na da ra’ayoyi daban-daban game da shugabancin Buhari, a wajen su mutumin kirki ne da ya wakilci garin su da ƙasa.

Gidan Sha’iskawa da ke Daura inda Buhari ya fito daga ciki na cike da mutane da ke nuna alhini, yayin da jami’an tsaro suka ci gaba da tsayuwa daram a gidan sa na GRA.

Makwabtan Buhari a Kaduna sun yi alhini

A Kaduna, inda Buhari ke da gida, maƙwabta da dama sun bayyana alhini da girgiza bisa mutuwarsa, suna addu’ar Allah ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu a London

Tsohon kansila a unguwar Sarki Kaduna, Zubairu Shanuna ya ce:

“Dukkanmu mutuwa za mu yi. Ina roƙon Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da Aljanna.”

Wani ɗan unguwar, Jafaru Jafaru Anaba, ya bayyana rasuwar Buhari a matsayin babban rashi ga ƙasa. Ya ce:

“Na ji matuƙar girgiza lokacin da na samu labarin. Gaskiya babban rashi ne ga ƙasa.”

Shugaban PDP na mazabar Kabala da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Shehu Isa Dan Inna, ya ce yana samun labarin mutuwar sai ya nufo gidan Buhari saboda girgiza da ya yi.

Buhari da mataimaki shi a fadar shugaban kasa
Buhari da mataimaki shi a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wani mai sayar da kayan masarufi a Chanranchi, Bello Idris Dalleje ya bayyana cewa har yanzu yana cikin ruɗani. Ya ce:

“Ko 'yan adawa na nuna alhini. Wannan ya nuna irin girman mutumin da ya rasu.”

Tarihi da wasu abubuwa kan Buhari

A wani rahoton, Legit Hausa ta yi waiwaye game da tarihin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Garba Shehu ya yi magana kan batun sa wa Buhari 'guba' a AC lokacin mulkinsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu bayan shafe shekara 82 a duniya sakamakon rashin lafiya da ya yi.

Muhammadu Buhari ya shugabanci Najeriya a lokacin mulkin soja kafin daga baya ya dawo siyasa ya yi wa'adi biyu, daga 2015 zuwa 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng