'An Yi Babban Rashi': Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Rasu, Ƴan Najeriya Sun Magantu
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibiti da ke London a ranar Lahadi, a cewar sanarwar Garba Shehu
- Garba Shehu ya ce Buhari ya dade yana jinya amma rashin lafiyarsa ba ta yi tsanani ba, sai kwatsam aka sanar da rasuwarsa
- 'Yan Najeriya sun aika sakonnin ta'aziyyarsu bisa rasuwar tsohon shugaban kasar tare da yi masa addu'ar samun rahamar Ubangiji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
London - Yanzun nan muke samun labarin cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu a asibitin da yake jinya a London.
Tsohon mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ne ya sanar da cewa Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yulin 2023.

Source: Facebook
Muhammadu Buhari ya rasu a London
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Garba Shehu ya ce:

Kara karanta wannan
London Clinic: An gano makudan kudi da ake biya kullum a asibitin da Buhari ya rasu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUUN.
"Iyalan tsohon shugaban kasar Najeriya sun sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar yau a wani asibitin London.
"Allah ya jikansa da Rahama, ya sa Aljannah Firdausi ce makomarsa."
Karanta sanarwar a nan kasa:
Rashin lafiyar Buhari kafin rasuwarsa
'Yan kwanakin da suka gabata ne Garba Shehu ya sanar da cewa Buhari ba shi da lafiya, amma yana samun sauki a wani asibitin London.
Garba Shehu ya bayyana cewa rashin lafiyar tsohon shugaban ƙasa mai shekaru 82 ba ta yi tsanani ba kamar yadda aka ruwaito.
Tsohon shugaban ƙasan ya jima yana fama da rashin lafiya, amma ana ganin yana samun sauƙi a a wancan lokacin, kamar yadda muka ruwaito.

Source: Twitter
'Yan Najeriya sun dimauce da rasuwar Buhari
'Yan Najeriya sun nuna kaduwarsu da suka samu labarin rasuwar tsohon shugaban kasar. Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin maganganun 'yan kasar:
@YahayaI28853208:
"Allah jikansa da Rahama."
@OwhePikin:
"Allah ya jikansa kamar yadda ya jikan 'yan Najeriya a lokacin da yake mulki."
@KenUttih:
"Allah ya jikansa da Rahama. Ya kamata mu rika aikata alheri. Rayuwar nan 'yar gajeriya ce. Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalansa."
@am_oluonye:
"Wannan abun bakin ciki ne sosai. Allah ya tausasa iyalansa."
@donpanacio:
"Lallai Najeriya ta yi babban rashi, Allah ya jikansa da Rahama. Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu."
@__victoh:
"Ga shi ya tafi ya barmu da lalatacciyar kasar da ya jawo lalacewarta."
@frank2zee:
"Ya kamata Tinubu da 'yan siyasa su dauki wa'azi daga irin wannan mutuwar. Rayuwar nan yau kai ne gobe ba kai ne ba. Da abin da ka shuka ne za a rika tunawa da kai."
Tinubu ya tura Shettima ya rako gawar Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar Muhammadu Buhari a Landan da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi.
Tinubu ya tattauna da Aisha Buhari don jajanta mata sannan ya umarci Kashim Shettima da ya rako gawar marigayin shugaban ƙasar.
Buhari ya taɓa mulki a matsayin shugaban soja da na farar hula, yayin da Tinubu ya umurta da a sauke tutoci domin girmama marigayin.
Asali: Legit.ng
