'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addinin Musulunci, Sun Bukaci N30m

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addinin Musulunci, Sun Bukaci N30m

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani malamin addinin Musulunci a jihar Eso da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
  • Miyagun sun sace malamin ne jim kaɗan bayan da ya kammala sallar Azahar a ranar Lahadi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa tuni har sun kira iyalansa inda suka nemi a ba su maƙudan kuɗaɗen fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Ƴan bindiga sun sace malamin addinin Musulunci a jihar Edo.

Ƴan bindigan sun sace babban limamin Uromi kuma shugaban ƙungiyar ɗalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) reshen Edo-Delta, Sheikh Murtadho Muhammad.

'Yan bindiga sun sace malamin addini a Edo
'Yan bindiga sun yi awon gaba da malamin addini a Edo Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an sace shi ne da a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace malamin addini a Edo

Lamarin ya faru ne kimanin ƙarfe 2:00 na rana a unguwar Angle 90 da ke garin Uromi, cikin ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun fara nuna wanda suke so jam'iyyar haɗaka ADC ta tsayar takara a 2027

Shaidu sun bayyana cewa an sace malamin ne jim kaɗan bayan kammala sallar Azahar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Rahotanni sun ce ya fita ne don siyan abinci ga iyalinsa, amma sai wasu suka tare shi suka tilasta masa shiga mota a kusa da gidansa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban majalisar ƙolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) reshen jihar Edo, Alhaji Abdulazeez Igbinidu, ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya kuma abin da ba za a yarda da shi ba.

Ya yi Allah-wadai da sace Sheikh Murtadho tare da kiran da a sako shi ba tare da wani sharaɗi ba.

Alhaji Abdulazeez ya buƙaci gwamnatin Edo da ta ɗauki matakan da suka dace don kare rayuwar ƴan ƙasa da kuma tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

“Ina jin suna neman kuɗi masu yawa sosai, mu kuma bamu da irin waɗannan kuɗin. Ko da kuwa kana da kuɗin, idan ka biya, ka na ƙarfafa musu guiwa ne."
"Gwamnati ce ke da dukkan kayan aikin tsaro. Saboda haka ya kamata su yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa an sako limamin cikin gaggawa, kuma ba tare da an cutar da shi ba."

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

"Ya kamata gwamnati ta ƙara zage damtse wajen tabbatar da cewa jama’a na iya kwanciya cikin kwanciyar hankali da yin ayyukansu cikin walwala ba tare da tsoron garkuwa ko kisan gilla ba."

- Alhaji Abdulazeez Igbinidu

'Yan bindiga sun sace malami a Edo
'Yan sun yi garkuwa da malamin Musulunci a Edo Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƴan bindiga sun buƙaci kuɗin fansa

Wata majiya daga cikin iyalan malamin ta bayyana cewa masu garkuwar sun riga sun tuntubi iyalinsa, inda suka nemi kuɗin fansa har Naira miliyan 30.

Lamarin ya tayar da hankalin al’ummar Musulmi a jihar, ganin matsayin Sheikh Murtadho a matsayin jagoran addini da kuma ɗaya daga cikin masu fafutukar cigaban matasa.

Dukkan ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar Edo ya ci tura, domin mai magana da yawun rundunar, CSP Moses Yamu, bai ɗaga kiran waya ba, kuma bai amsa saƙon da aka aika masa ba.

Ƴan bindiga sun kashe fasinjoji a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan matafiya a jihar Zamfara.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka fasinjoji aƙalla bakwai bayan sun buɗewa motar da suke ciki wuta.

Hakazalika sun kuma yi awon gaba da wasu fasinjojin da ke cikin wasu motoci daban a yayin harin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng