Atiku Ya Sake Taso Shugaba Tinubu a Gaba kan Cire Tallafin Man Fetur
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi kalamai masu kaushi kan Shugaba Bola Tinubu
- Atiku ya soki Shugaba Tinubu kan matakin da ya ɗauka na cire tallafinan fetur a ranar farko ta hawansa kan kujerar mulki
- Ya bayyana cewa wannan matakin da Tinubu ya ɗauka, ya jefa ƴan Najeriya cikin halin ƙaƙanikayi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, caccaki Shugaba Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur.
Atiku ya ce matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin fetur a ranar farko da ya hau mulki ne ya jefa ƙasar nan cikin mawuyacin halin tattalin arziƙi da ake fama da shi a yau.

Source: Facebook
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin wata rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan
2027: Malamin addini ya ja kunnen Tinubu, ya fadi abin da zai kawo masa cikas kan tazarce
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya soki Shugaba Tinubu
Atiku ya bayyana wannan matakin da cewa "gaggawa ne da rashin tunani", yana mai ƙara da cewa hakan ya tilasta talakan Najeriya fama da nauyin hauhawar farashi da yunwa.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da karya alƙawarin da ta ɗauka na rage wa ma’aikatan tarayya raɗaɗin cire tallafin ta hanyar bayar da wani albashi na wucin gadi.
"A cikin yunƙurin da gwamnati ke yi don daidaita rikicin da ta jawo wa kanta, ta yi alkawarin biyan wani ƙari na albashi ga ma’aikatan tarayya a matsayin rage radadi na ɗan lokaci, har zuwa lokacin da za a kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa."
“Wannan alkawari kamar yadda ya saba a ƙarƙashin wannan gwamnati, ya zama wani abu da aka kasa cikawa."
- Atiku Abubakar
Atiku ya ragargaji gwamnatin Tinubu
Atiku ya yi nuni da cewa ya ɗauki gwamnati watanni 10 kafin ta cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi, kuma a wannan lokacin ne ake tsammanin a riƙa biyan ƙarin albashi a matsayin cike gurbi.

Kara karanta wannan
Rikici ya ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari, an fara musayar yawu kan zaben 2015
"A takaice, gwamnatin tarayya tana da bashi na watanni 10 na ƙarin albashi da ya kamata ta biya ma’aikatan tarayya. Amma har yanzu watanni shida ne kacal aka biya, kuma bayan jinkiri da alƙawuran da ba a cika ba."
- Atiku Abubakar

Source: Facebook
Ya bayyana cewa kowane ma’aikaci yana da hakkokin Naira 35,000 a wata har na tsawon watanni huɗu, wanda ya kai jimillar Naira 140,000 ga kowanne mutum.
Atiku ya yabawa wasu gwamnonin jihohi da suka gudanar da lamuran ma’aikata cikin sanin ya kamata, amma ya soki gwamnatin tarayya bisa nuna halin ko in kula da raina ƴan ƙwadago.
Har wa yau, ya la’anci cigaba da tsare Andrew Uche Emelieze, wani mai rajin kare hakkokin ma’aikata, wanda aka kama kimanin makonni biyu da suka gabata saboda yunƙurin shirya zanga-zangar lumana kan batun albashin da ba a biya ba.
Tinubu ya dawo Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga dawo gida Najeriya bayan ya ziyarci ƙasashe biyu.
Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya ne a daren ranar Asabar bayan ya kai ziyara a ƙasashen Saint Lucia da Brazil.
Bayan dawowarsa gida, Shugaba Tinubu ya samu tarba daga wajen manyan jami'an gwamnati.
Asali: Legit.ng