'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Fafata da Jami'an 'Yan Sanda, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Fafata da Jami'an 'Yan Sanda, an Samu Asarar Rayuka

  • Jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Kebbi sun yi artabu da ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa masu tayar da ƙayar baya
  • Ƴan ta'addan sun yi yunƙurin tare matafiya ne a kan titin Zogirma zuwa Tilli lokacin da jami'an tsaron suka yi artabu da su
  • A yayin artabun da ya biyo, an hallaka ƴan ta'adda masu yawa tare da raunata wasu, yayin da suka kashe jami'an ƴan sanda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Mambobin ƙungiyar ƴan ta'addan Lakurawa sun kashe jami'an tsaro na ƴan sanda a jihar Kebbi.

Ƴan ta'addan na Lakurawa sun kashe ƴan sandan ne guda uku da yammacin ranar Juma’a a garin Zogirma da ke ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi.

'Yan Lakurawa sun kashe 'yan sanda a Kebbi
'Yan sanda sun fafata da 'yan Lakurawa a Kebbi Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

'Yadda Buhari ya ki karbar sababbin motocin N400m a Villa', Garba Shehu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun fafata da ƴan Lakurawa

Kakakin ƴan sandan ya ce wata haɗakar tawagar ƴan sanda ta fafata da waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar Lakurawa ne a musayar wuta mai zafi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya ce jami'an tsaron sun fafata da ƴan ta'addan na Lakurawa ne a yayin da suka yi ƙoƙarin kai hari ga matafiya da ke bin hanyar Zogirma zuwa Tilli.

"Sakamakon hakan, an hallaka wasu daga cikin ta'addan da ake zargin ƴan Lakurawa ne, yayin da wasu suka tsere cikin daji ɗauke da munanan raunuka."
"Abin takaici, ƴan sanda uku masu jarumtaka sun rasa rayukansu a yayin fafatawar."

- DSP Nafiu Abubakar

Ya ƙara da cewa, DPO na Zogirma ya hanzarta haɗa tawagar ƴan sanda tare da samun ƙarfafawa daga rundunar Mobile Police ta 36 da ke Birnin Kebbi, amma ƴan ta'addan sun gudu zuwa dajin da ke kusa.

An yabawa jami'an ƴan sanda

Kara karanta wannan

2027: Na kusa da Tinubu ya yi maraba da kafa hadaka, ya faɗi amfaninta ga Najeriya

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya yaba da jajircewa, jarumtaka da ƙoƙarin da waɗanda suka rasa rayukansu suka nuna, inda ya yi addu’ar Allah ya jikansu da rahama ya sa sun huta.

'Yan Lakurawa sun kashe 'yan sanda
'Yan ta'addan Lakurawa sun yi artabu da 'yan sanda a Kebbi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su kasance cikin shiri da faɗakarwa, tare da gaggauta kai rahoton duk wata alama ko motsi da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa.

CP Bello M. Sani ya sake nanata ƙudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Ƴan bindiga sun kashe matafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'adda ɗauke da makamai sun kai farmaki kan matafiya a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ƴan bindigan sun hallaka fasinjoji bakwai bayan sun buɗewa motarsu wuta a kan hanyar Gusau zuwa Funtua da ke Zamfara.

Hakazalika ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu fasinjojin bayan sun tare motoocinsu a kan hanyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng