Katsina: Bayan Ƙorafin Fulani, Gwamna Ya Dakatar da Sarki, Jami'an Gwamnati

Katsina: Bayan Ƙorafin Fulani, Gwamna Ya Dakatar da Sarki, Jami'an Gwamnati

  • Gwamnatin Katsina ta dakatar da wasu jami’an gandun daji da hakimin kauye saboda zargin mamaye dazuka da filayen kiwo a Ingawa
  • Kungiyar Kautal Ja’onde Jam ta kai korafi kan yadda ake mamaye hanyoyin dabbobi da filayen kiwo, lamarin da ke haddasa rikici da manoma
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya umarci gudanar da bincike tare da ladabtar da duk wanda aka samu da laifi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta dakatar da wasu jami’an gandun daji da wani basaraken gargajiya.

Gwamna Dikko Umaru Radda shi ya dauki wannan mataki saboda zargin mamaye daji a Karamar Hukumar Ingawa.

Gwamnan Katsina ya dakatar da basarake
Gwamna Radda ya dakatar da basarake a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Rassa.
Source: Facebook

An dakatar da Sarki da jami'an gwamnatin Katsina

An ɗauki matakin ne bayan kungiyar Fulani mai suna Kautal Ja’onde Jam ta kai ƙorafi kan mamaye hanyoyin kiwo da dazuka da wuraren kiwo, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hana Fulani makiyaya kiwo a jiharsa, ya ba su wa'adin kwana 12 kacal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce wannan al’amari yana shafar makiyaya kuma yana barazanar haifar da rikici da manoma masu zaman kansu a yankin.

Wani kwamitin bincike na farko da Sakataren Gwamnatin Jiha, Abdullahi Faskari da jami’an tsaro suka jagoranta ya tabbatar da zargin.

Kwamitin ya gano cewa an sare ɓangare na dajin Bai a kauyen Manomawa don noma a bana.

Binciken ya kuma gano abubuwan da suka nuna an samu rashin bin ka’ida wajen rabon filaye, ciki har da rawar da hakimin kauyen ya taka.

An bayyana sunan shugaban gandun daji na yankin Kankia, Shuaibu Gambo, da shugaban sashen gandun daji na Ingawa, Saidu Danjuma.

Saboda haka, Gwamna Dikko Radda ya amince da ɗaukar matakai don hana tashin hankali da yawan rikice-rikicen da suka shafi filaye.

Gwamnan Katsina ya dakatar da Sarki bayan korafin Fulani
Gwamna Radda ya dakatar da Sarki da wasu jami'an gwamnati a Katsina. Hoto: Legit.
Source: Original

Umarnin da gwamnatin Katsina ta bayar

A cewar wata sanarwa daga gwamnati, matakan sun haɗa da dakatar da shugaban gandun dajin a Kankia da kuma gudanar da cikakken bincike.

Kara karanta wannan

Adamawa: Gwamna Fintiri ya ƙaƙaba dokar hana fita bayan ɓarkewar rikici

Sanarwar ta ce:

“An bukaci dakatar da shugaban gandun daji na Kankia da wanda ke kula da Ingawa, an umarci Ma’aikatar Muhalli ta jiha da ta gudanar da bincike cikakke kan ayyukan jami’in Kankia da daukar matakin ladabtarwa.
“An bukaci Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta binciki shugaban sashen Ingawa da ɗaukar matakin ladabtarwa.
"Ana son Majalisar Masarautar Katsina da ta binciki rawar da hakimin Manomawa ya taka da kuma ɗaukar matakin da ya dace.”

Gwamnatin Dikko Umaru Radda ta ce za ta ci gaba da kare dukiya da albarkatun al’umma tare da tabbatar da gaskiya da adalci a duk matakan gwamnati.

Ta kuma lashi takobin ɗaukar matakin da ya dace kan duk wani abu da zai iya haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Gwamna Radda ya kalubalanci hadakar yan adawa

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Katsina ya kalubalanci Atiku Abubukar, Peter Obi da sauran ƴan haɗakar ADC kan batun tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Turawa sun zakulo Abba Kabir cikin gwamnoni, an karrama shi a London

Dikko Umaru Raɗɗa ya nuna cewa ba ta yadda jagororin adawa za su iya dawo da tallafin kuma su tafiyar harkokin gwamnati.

Gwamnan ya buƙaci ƴan haɗaka su fito su yi wa ƴan Najeriya bayanin abin da za su yi wanda ba shi Tinubu ke yi ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.