Ana tsaka da Rikicin Sarautar Kano, An ga Sarki Sanusi II da Wasu Manyan Mutane a Ingila
- Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya halarci gasar wasan polo da bankin Access ya saba shiryawa duk shekara a ƙasar Ingila
- A wurin wannan taro, Sarki Sanusi II ya haɗu da tsohon ƙocin ƙungiyar kwallon ƙata ta Chelsea kuma kocin tawagar Ingila, Thomas Tuchel
- Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan harin da aka kai Fadar Sarki Sanusi II da ke Ƙofar Kudu a kwanakin da suka shige
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
England - Yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan sarautar Kano, Mai Martaba Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II ya halarci wurin wasan Polo a ƙasar Ingila.
Khalifa Muhammad Sanusi II, ya halarci gasar wasan polo ta Access Bank na 2025 wanda aka gudanar a filin Guards Polo Club da ke Surrey, Ingila.

Source: Twitter
Masarautar Kano ta tabbatar da hakan a wani gajeren sako mai haɗe da faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na X yau Asabar, 12 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya halarci gasar wasan Polo a Ingila
Sanarwar ta ce wannan taro ya tara manyan baki daga sassa daban-daban na duniya, domin bikin wasanni, al'adu, da diflomasiyya.
"Mai Martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, ya halarci gasar wasan polo ta Access Bank ta 2025 wanda aka yi a filin wasa Guards Polo Club da ke Surrey, Ingila.
"Wannan taro ya tara manyan baki daga sassa daban-daban na duniya domin bikin wasanni, al'adu, da diflomasiyya," in ji sanarwar.
Sarkin Kano ya haɗu da kocin Ingila, Thomas Tuchel
Northern Fact Zone ta wallafa a X cewa Sanusi II ya gana da kocin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Ingila, Thomas Tuchel a wurin gasar ƙwallon polo yau Asabar.

Kara karanta wannan
Aminu vs Sanusi: Rikicin sarautar Kano na neman dawowa ɗanye, an aika saƙo ga Kotun Ƙoli
An ga basaraken yana tattaunawa da Tuchel, tsohon kocin kungiyar Chelsea da ke buga gasar kofin Firimiya na Ingila a wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

Source: Twitter
Sai dai har yanzu ba a bayyana abin da Sarki Sanusi ya tattauna da Thomas Tuchel ba, wasu na ganin gaisawa kawai suka yi.
Sanarwar ta ce:
"Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II, PhD, CON, ya gana da tsohon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea kuma kocin tawagar Ingila, Thomas Tuchel, a birnin Landan, yau Asabar, 12 ga Yuli, 2025.
An nemi kotun koli ta warware rikicin Kano
A wani labarin, mun kawo maku cewa wata ƙungiya ta buƙaci kotun kolin Najeriya ta gaggauta yanke hukuncin da zai kawo ƙarshen rikicin sarautar Kano da ake fama da shi.
Kano na fama da rikicin sarauta ne tun bayan dawo da Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Abba Kabir ta yi, tare da rusa masarautu biyar da Ganduje ya kirƙiro.
Ƙungiyar ta bayyana cewa rikicin Aminu Ado da Sanusi II ya raba kan jama’ar Kano tun daga siyasa da biyayya ga masarauta, wanda hakan ke ƙara dagula yanayin zamantakewa.
Asali: Legit.ng
