2027: Na Kusa da Tinubu Ya yi Maraba da Kafuwar Hadaka, Ya Fadi Amfaninta ga Najeriya

2027: Na Kusa da Tinubu Ya yi Maraba da Kafuwar Hadaka, Ya Fadi Amfaninta ga Najeriya

  • Femi Gbajabiamila ya fito ya yi magana kan haɗakar jam'iyyun ƴan adawa da ke ƙarƙashin jam'iyyar ADC
  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasan ya bayyana cewa haɗakar abu ne wanda za a yi maraba da shi
  • Tsohon kakakin majalisar wakilan ya nuna cewa tsarin dimokuraɗiyya ya fi kyau idan akwai adawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Femi Gbajabiamila, ya yi magana kan haɗakar ƴan adawa.

Femi Gbajabiamila ya bayyana haɗakar shugabannin jam’iyyun adawa cikin jam’iyyar ADC a matsayin wani ci gaba mai kyau da zai hana Najeriya faɗawa cikin tsarin jam’iyya ɗaya tilo.

Gbajabiamila ya yi magana kan hadaka
Femi Gbajabiamila ya yi maraba da kafa hadaka Hoto: @SpeakerAbbas, @ADCNg
Source: Twitter

Gbajabiamila ya bayyana haka ne bayan ya kada ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomi na jihar Legas da aka gudanar a Surulere, ranar Asabar, cewar rahoton jaridar TheCable.

Me Gbajabiamila ya ce kan haɗaka?

Kara karanta wannan

ADC ta ɓullo da sabon tsari, ta gindaya wa Atiku, Obi da Amaechi sharaɗin neman takara a 2027

Sai dai ya bayyana rashin tabbas game da makomar haɗakar wacce Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan ƴan adawa suke jagoranta.

Ya nuna cewa wannan haɗakar ba ita ba ce ta farko da aka taɓa yi a Najeriya ba.

"Ci gaba ne mai kyau dangane da wannan haɗakar. Ba wannan ne karon farko da muke ganin irin haka ba. To amma dai, ci gaba ne mai kyau."
“A kowace dimokuraɗiyya, dole sai an samu wani matakin adawa, idan ba haka ba za mu faɗa cikin tsarin jam’iyya ɗaya tilo. Amma ban da tabbacin inda hakan zai kai ba."

- Femi Gbajabiamila

An yi zaɓen ƙananan hukumomi a Legas

Yayin da yake magana kan yadda aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya bayyana zaɓen a matsayin mai cike da kwanciyar hankali, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Femi Gbajabiamila dai ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe ta PU 014 dake makarantar sakandare ta Elizabeth Fowler Memorial a unguwar Adeniran Ogunsanya a Surulere

Femi Gbajabiamila ya yi maraba da hadaka
Femi Gbajabiamila ya yaba da zaben kananan hukumomin Legas Hoto: @FemiGbaja
Source: Twitter
"Har yanzu abin da na gani shine zaman lafiya, shiru da lumana, kuma zaɓe mai ƴanci da adalci. Na ɗan ji takaici kaɗan saboda rashin fitowar jama’a, wannan ne ɓangaren da ya kamata mu yi aiki a kai. Jama’a ba sa fitowa sosai bisa ga abin da na gani."

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fadi shirinta kan masu burin takarar shugaban kasa

“Watakila saboda mutane ba su fahimci muhimmancin zaɓen ƙananan hukumomi sosai ba ne, alhali kuwa wannan ne mafi muhimmanci fiye da sauran zaɓe."
"Dole ne mu wayar wa mutane kai. Dole ne mu ilmantar da su kan muhimmancin gwamnatin da ke a matakin kusa da jama'a."
“Amma dai har zuwa yanzu, komai lafiya lau, babu hayaniya, babu tarzoma. Zaɓen ya kasance na gaskiya da adalci. Wannan shi ne abin da muke so a kowane zaɓe."

- Femi Gbajabiamila

Sanata Ireti Kingibe ta koma ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa ta koma jam'iyyar ADC ta.ƴan haɗaka.

Sanata Ireti Kingibe ta koma tafiyar ƴan haɗaka ne bayan ta sanar da ficewa daga jam'iyyar LP mai adawa.

Ta bayyana cewa ta fice daga jam'iyyar LP saboda rikicin da ya addabe ta wanda ya jawo ta dare zuwa gida biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng