Gwamna Ya Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Jiharsa, Ya ba Su Wa'adin Kwana 12 Kacal

Gwamna Ya Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Jiharsa, Ya ba Su Wa'adin Kwana 12 Kacal

  • Gwamnatin jihar Imo ta kakaba wata doka ga makiyaya a fadin jihar domin dakile matsalolin da ake samu na rashin tsaro
  • Gwamnatin ta ba makiyaya wa'adi zuwa 24 ga Yuli 2025 su daina kiwon shanu a fili domin tabbatar da zaman lafiya da doka
  • Kwamishinan bunkasa kiwon dabbobi, Dr. Mgbeahurike, ya ce gwamnati ba za ta yarda da kiwon da ke haifar da rikici da barna ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Gwamnatin Jihar Imo ta ba makiyaya umarni a fadin jihar domin kawo karshen matsalolin da ake samu.

Gwamnatin Hope Uzodinma ta dakatar da kiwon shanu a fili kafin ko zuwa 24 ga Yuli, 2025 da muke ciki a fadin jihar.

Gwamna ya hana kiwo barkatai a jiharsa
Gwamna Uzodinma ya hana Fulani makiyaya kiwo barkatai a Imo. Hope Uzodinma.
Source: Facebook

Sanarwar ta fito daga Kwamishinan Raya Kiwo, Dr. Anthony Mgbeahurike wanda ya fitar ga manema labarai, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sokoto: Gwamnati ta kafa sharuɗa masu tsauri ga Turji yayin da ake maganar sulhu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya magantu game da Fulani a jiharsa

Sai dai Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a yankin Kudu maso Gabas.

Soludo ya bayyana ba Fulani makiyaya ba ne ke aikata laifukan satar mutane da kashe-kashe a yankin ba.

Ya ɗora alhakin aikata laifukan da suka shafi garkuwa da mutane da kashe-kashe a kan ƴan ƙabilar Igbo.

Abin da gwamnatin Imo ta ce

Mgbeahurike ya bayyana haka ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da makiyaya a Owerri, babban birnin jihar.

Dr. Mgbeahurike ya ce gwamnati na kokarin ganin an samu zaman lafiya da daidaiton tattalin arziki tsakanin manoma da makiyaya.

Ya ce:

“Gwamnati ta bayar da tallafi a baya, ciki har da rigakafin cutar 'anthrax' kyauta, amma ba za mu yarda da kiwo barkatai ba.”
Gwamna ya hana Fulani kiwo a fili
Gwamnan Imo ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwana 12 su bar kiwo barkatai. Hoto: Legit.
Source: Original

Musabbabin daukar matakin dakile kiwo barkatai

Kara karanta wannan

Adamawa: Gwamna Fintiri ya ƙaƙaba dokar hana fita bayan ɓarkewar rikici

Ya jaddada cewa makiyaya su guji lalata gonaki, kuma idan haka ta faru, za su biya diyya cikin gaggawa da adalci, cewar rahoton Leadership.

A wani bangare na tsarin doka, gwamnati ta tabbatar da Alhaji Shuaibu a matsayin sabon shugaban makiyaya a jihar.

Dr. Mgbeahurike ya umurce shi da tabbatar da cewa duk makiyaya sun bi doka game da hana kiwo a fili.

Alhaji Shuaibu ya gode wa gwamnati, ya ce sun fahimci matsalolin da kiwo a fili ke haddasawa kuma za su bi doka.

Ya ce:

“Muna da niyyar yin aiki da gwamnati, za mu isar da wannan umarni ga makiyaya don tabbatar da tsafta da zaman lafiya.”

Gwamnati ta sake nanata cewa za a aiwatar da wannan sabon tsarin doka da tsauri bayan karewar wa'adin da aka bayar.

Imo: Gwamna Uzodinma ya kori Kwamishinan Shari'a

Kun ji cewa Gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC mai mulki, Hope Uzodinma ya sallami Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da dabaru na jihar Imo, Cif Declan Emelumba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 26 ga watan Mayu.

Sanarwar ba ta faɗi dalilin da ya sa gwamnan ya kori kwamishinan ba amma wata majiya daga gidan gwamnati ta ce Uzodinma na da iko naɗawa ko saukewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.