'A Shirye na Taho Daman': Ɗan Bello Ya Faɗi Abin da Ya Faru bayan Cafke Shi a Kano

'A Shirye na Taho Daman': Ɗan Bello Ya Faɗi Abin da Ya Faru bayan Cafke Shi a Kano

  • Jami’an DSS sun kama Ɗan Bello a filin jirgin sama na Kano, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a
  • A cewar Ɗan Bello, jami’an sun karɓi fasfonsa da kayansa kafin su tafi da shi, amma daga baya suka sake shi
  • Ɗan Bello ya ce bai yi mamakin kame shi ba, yana kira ga jama’a da su kwantar da hankali, yana cikin koshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wasu jami’an DSS sun kama Ɗan Bello, shahararren mai barkwanci a kafafen sada zumunta, a filin jirgin saman Kano bayan isowarsa Najeriya.

An ce jami’an sun karɓi kayansa da fasfo, suka tafi da shi, lamarin da ya ja hankalin fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin sosai.

Dan Bello ya yi magana bayan sakinsa da aka yi
Dan Bello ya fadi shirinsa kafin shigowa Najeriya. Hoto: Dan Bello.
Source: Facebook

Dan Bello ya magantu bayan an kama shi

Kara karanta wannan

Abin da ya faru bayan jami'an tsaro sun kama Ɗan Bello a filin jirgi a Kano

Ɗan Bello ya yi magana bayan an sake shi yayin jira da jaridar DCL Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya tabbatar da labarin inda ya ce yana sauka a filin jirgin sama a Kano wasu mutane suka kama shi bayan karbe fasfo dinsa.

Dan Bello ya ce:

“Dana sauko wasu mutane wanda kana ganinsu ka san hukumomi ne suka karɓi fasfo da sauran kayayyakina.
“Suka ce ga mota nan na hau mu tafi, sai ga barista Abba Hikima nan, aka shiga doguwar tattaunawa cikin turanci.”
Dan Bello ya magantu bayan cafke shi da aka yi
Dan Bello ya fadi abin da ya faru yayin da aka cafke shi. Hoto: Dan Bello.
Source: Facebook

Menene dalilin cafke Dan Bello a Kano?

Bayan kusan awa ɗaya da rabi ana magana, jami’an suka sake shi, ya tabbatar da cewa an sake shi.

Wasu da shaidun gani da ido sun ce jami’an sun kama shi daga Abuja ba tare da bayyana dalili ba, lamarin da ya ta da hankali.

Wata majiya ta tabbatar da cewa DSS ne suka kama shi, amma daga baya suka sake shi, watakila an ba su sababbin umarni ne.

Majiyar ta ce:

Kara karanta wannan

Mummunan iftila'i ya sauka kasar Amuka, mutane 120 sun mutu, an nemi 160 an rasa

“Lallai DSS ne suka kama shi, amma sun sake shi daga baya. Wataƙila sun samu sabon umarni ne don a sake shi.”

Shirin da Dan Bello ya yi kafin dawowa

Dan Bello ya ce ai ya san yadda Najeriya ta ke kuma a shirye ya zo saboda ya san komai na iya faruwa.

Dan Bello ya ce:

“A Najeriya muke da, Har da kayan gidan yarina na taho a shirye, ban yi mamakin kama ni ba.
“Ina son mutane su kwantar da hankalinsu, ina lafiya sannan Allah Ya ƙara mana kwanciyar hankali mu saita ƙasarmu.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwa ba, kuma ba a bayyana dalilin kama Ɗan Bello ba.

Dan Bello ya dura kan gwamnatin Tinubu

Kun ji cewa Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fito ya ƙara yi wa shugaba Bola Tinubu wankin babban bargo.

Dan Bello ya bayyana cewa ƴan Najeriya na fama da yunwa saboda tsare-tsaren da gwamnati mai ci ta kawo.

Ya ƙalubalanci gwamnati da ta shigar da shi ƙara a kotu idan har ba ta jin daɗin wayar da kan jama'an da yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.