2027: Malamin Addini Ya Ja Kunnen Tinubu, Ya Fadi Abin da Zai Kawo Masa Cikas kan Tazarce
- Primate Elijah Ayodele ya bi sahun masu aika saƙon gargaɗi ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan zaɓen shekarar 2027
- Malamin addinin na Kirista ya ja kunnen shugaban ƙasan kan ya yi taka tsan-tsan da gwamnonin da suke sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
- Ya nuna cewa akwai mutanen da ke cikin gwamnatinsa waɗanda suke son ganin bayansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi gargaɗi ga shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Primate Ayodele ya gargaɗi Tinubu ne game da wasu daga cikin mutanen da ya naɗa muƙamai da kuma gwamnoni daga jam’iyyun adawa da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokon yaɗa labarai ya fitar.

Kara karanta wannan
Wace irin cuta ta kama Ganduje? An tsokani tsohon gwamnan Kano bayan ya karɓi muƙami a FAAN
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Primate Ayodele ya yi gargaɗi ga Tinubu
Malamin addinin ya bayyana cewa mutanen abokan gaba ne kuma za su yi aiki da nufin kawar da shi.
Primate Ayodele ya kuma yi gargaɗi ga Shugaba Tinubu kan tattalin arzikin Najeriya, matsalolin tsaro, da sauran batutuwa.
Ya gargaɗi Tinubu da ya yi taka-tsantsan, yana mai cewa za a yi amfani da rashin tsaro don hana shi samun wa’adin mulki na biyu.
Ya kuma bayyana cewa akwai wasu mutane a cikin gwamnatinsa, har da waɗanda ke cikin fadar Aso Rock da suke da hannu a cikin rikicin tsaro.
Malamin ya kuma shawarci jami’an tsaro da su yi hattara da zuwan watan Oktoba, inda ya ce matsalolin tsaro za su ƙaru matuƙa. Ya kuma buƙaci shugaban ƙasa da ya rage farashin kayan abinci.
"Tinubu ya yi taka-tsantsan, za su yi amfani da rashin tsaro don hana shi wa’adin mulki na biyu. Ya yi ƙoƙari sosai wajen rage farashin kayan masarufi, amma wahala na nan."
"Matsalar tsaro na nan, akwai wasu a cikin rundunonin sojoji da hukumomin tsaro, har ma da fadar gwamnati da ke da hannu."
- Primate Ayodele
Primate Ayodele ya kuma yi gargaɗi ga Tinubu da kada ya yi kuskure wajen zaɓen shugaban APC na gaba domin hakan na iya sa jam’iyyar ta durƙushe.
Ya kuma roƙi sojoji da su ƙara ƙaimi wajen hana fashewar bama-bamai, yana mai cewa wannan wata dabara ce don tayar da zaune tsaye a gwamnati.

Source: Facebook
An ja kunnen Tinubu kan gwamnoni
A ci gaba da jawabin nasa, Primate Ayodele ya kuma yi gargaɗi ga Tinubu da kada ya yarda da gwamnoni da suka sauya sheƙa zuwa APC, saboda wasu daga cikinsu za su yi masa zagon ƙasa.
"Kada ka yarda da waɗannan gwamnoni, ba duka suke ƙaunarka ba, kuma ba duka suka zo gare ka saboda ƙauna ba; niyyarsu ba ta da tsabta. Dole ka yi taka-tsantsan sosai."
"Har yanzu ba ka fahimta ba. Wasu daga cikin maƙiyanka suna samun muƙamai a cikin gwamnatinka, kuma mafi yawan ’yan kasuwa da kake dogaro da su za su juya maka baya."

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun kunyata haɗakarsu Atiku, sun hango wanda ya dace da Najeriya a 2027
- Primate Ayodele
Abin da Tinubu ya ce kan Buhari dangane da 2023
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai magana da yawun bakin Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi kalamai kan zaɓen 2023.
Garba Shehu ya ce mai girma Bola Tinubu ya yaba kan yadda Buhari ya bari aka yi gaskiya da adalci a zaɓen.
Ya ce Shugaba Tinubu ya nuna cewa adalcin da Buhari ya bari aka yi ne ya sanya ya samu nasara a zaɓen.
Asali: Legit.ng
