'Yan Bindiga Sun Kashe Matafiya a Zamfara, an Yi Awon da wasu Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Kashe Matafiya a Zamfara, an Yi Awon da wasu Masu Yawa

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa kan matafiya a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka fasinjoji bakwai bayan sun buɗe wa motarsu wuta lokacin da suke tafiya
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun zo tsallaka titi ne lokacin da suka buɗe wuta ga motar wacce ke kan hanyar Gusau-Funtua

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka aƙalla fasinjoji bakwai a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun jikkata wasu da dama a harin da suka kai ranar Alhamis, lokacin suka bude wuta kan wata motar haya a kan hanyar Tsafe-Funtua da ke jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun hallaka matafiya a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, kafin a rufe hanyar a yinin wannan ranar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Nasarawa, an samu asarar rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kashe fasinjoji

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ƴan bindigan waɗanda ke kan babura sun zo tsallaka hanyar ne lokacin da suka hango motar sannan suka buɗe mata wuta.

"Suna tafiya a hanyar su ne a lokacin da suka hango motar, suka fara harbi nan take. Motar na ɗauke da mata da yara. Mutum bakwai, ciki har da wasu yara, suka mutu a wurin."

- Wata majiya

Wata majiyar daban ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji daga wasu motocin biyu daban an sace su a yayin harin.

Wani jagoran al'umma a ƙaramar hukumar Tsafe, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa motar ta sauka daga hanya, ta faɗa cikin daji kuma ta kife sakamakon harin.

“Mun samu labari cewa direban na ƙoƙarin isa Gusau kafin a rufe hanyar ne. Wataƙila da ya kwana a Funtua, hakan da bai faru ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 400 sun kai hari a Kebbi, an yi gumurzu da dakarun sojoji

- Wani jagoran al’umma

Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin gwamnati na Tsafe domin kula da su.

'Yan bindiga sun kashe matafiya a Zamfars
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta yi ƙoƙarin tuntubar mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa bai samu wani rahoto makamancin hakan ba, inda ya yi mamaki kan rahoton harin.

"Gaskiya ban samu wani rahoton wani lamari makamancin haka ba. Sai dai ban sani ba ko a Funtua aka yi, amma mu gaskiya hanyarmu ta yi lafiya sosai."

- DSP Yazid Abubakar

Jami'an tsaro sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi yunƙurin karɓe iko da garin Ribah a jihar Kebbi.

Dakarun sojoji sun kai agajin gaggawa inda suka fafata da ƴan bindigan da suka zo kan babura waɗanda yawansu ya wuce mutum 400.

Sojojin sun hallaka ƴan bindiga da dama a yayin fafatawar wacce ta auku a ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng