Garba Shehu Ya Fadi Dan Takarar da Buhari Ya Fi So a Zaben 2023
- Garba Shehu, tsohon mai ba tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kai, ya yi tsokaci kan zaɓen shekarar 2023
- Garba Shehu ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Buhari bai da ɗan takara da ya fi so ko ya fi bai wa fifiko a zaɓen da ya gabata
- Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasan ya bayyana yadda Buhari ya yi mu'amala da dukkan ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Garba Shehu ya yi magana kan yadda Muhammadu Buhari ya mu'amalanci ƴan takarar shugaban ƙasa na APC a zaɓen 2023.
Tsohon mai taimakawa shugaban ƙasan ya ce babu wani ɗan takara da Buhari ya ƙi karɓarsa ko ya nuna rashin goyon baya gare shi a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan
Garba Shehu ya fadi halin da Buhari yake ciki bayan kwantar da shi a asibitin Landan

Source: UGC
Garba Shehu a bayyana hakan ne a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Television da aka watsa a ranar Juma’a, 11 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalamansa sun zo ne yayin da ake tattaunawa kan wanda Buhari ya fi so a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Buhari ya yi maraba da kowane ɗan takarar APC
Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari ya bai wa duk wanda ya zo wajensa da niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC wata shaida ta “ba a ƙi ka ba”.
"Ya bai wa kowa da ya je wajensa shaida ta 'ba a ƙi ka ba.'"
- Garba Shehu
Mai magana da yawun Buhari ya bayyana cewa wannan salon na Buhari ya dace da furucinsa na cewa: "Ni na kowa ne, amma ba mallakin kowa ba ne."
Buhari ya tsaya a kan kalamansa
Garba Shehu ya ƙara da cewa mutane da dama sun riƙa ambaton sunayen wasu ƴan takara a matsayin waɗanda Buhari ya fi so, amma tsohon shugaban ƙasan da kansa bai taɓa ambaton wani ɗan takara ba.

Kara karanta wannan
Rikici ya ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari, an fara musayar yawu kan zaben 2015

Source: Twitter
Ya kuma amince da maganar mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, wanda ya ce Buhari ya faɗa a baya cewa idan ya bayyana wanda ya fi so, wataƙila a kashe mutumin.
"Ya tsaya tsayin daka kan gaskiya. Bai nemi tilasta wani ra'ayi ba, ya ce jam’iyya ce za ta yanke shawara. Mun fitar da bayani a wancan lokacin, kuma abubuwa sun tabbatar da hakan."
"Waɗanda ke ta ambaton sunaye za su iya cewa komai kuma su danganta da Buhari, amma ba shi da kansa ba."
- Garba Shehu
'Buhari na samun sauƙi' - Garba Shehu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Garba Shehu tsohon mai magana da yawun bakin Muhammadu Buhari, ya taɓo batun rashin lafiyar tsohon shugaban ƙasan.
Garba Shehu ya ba da tabbacin an sallami tsohon shugaban ƙasan bayan an kwantar da shi a wani asibiti da ke birnin Landan.
Hakazika ya nuna cewa rashin lafiyar Buhari bai yi tsanani ba kamar yadda ake yayatawa a cikin rahotanni.
Asali: Legit.ng