'Har Aron Riga Mun ba Shi': Wani da Aka Kora a Fada Ya Faɗi Halaccin da Suka Yiwa Sanusi II
- Ana zargin Sarki Sanusi II da bayar da umarnin korar wasu masoyan Aminu Ado Bayero daga fadar Sarki saboda rashin biyayya
- A wani bidiyo, Sani Kwano ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta taimaki Sanusi II fiye da yadda danginsa suka taba kula da shi
- Kwano ya ce su fiye da mutum 200 ne a gidan Sarki, kuma ba duka suke adawa da Sanusi ba, wasu suna tare da shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ana cigaba da jefa maganganu bayan korar wasu masoyan Aminu Ado Bayero a fadar Sarki.
Ana zargin Sarki Muhammadu Sanusi II da umartar a kori masoyan Aminu Ado saboda rashin biyayya.

Source: Facebook
An koka kan butulcin da aka a fadar Sanusi
Wani daga cikin wadanda aka kora ya yi bayani a faifan bidiyo da shafin Masarautar Kano ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Muhammad Sani Kwaru (Sani Kwano) ya koka kan rashin mutunci da aka musu.
Sani Kwano ya yi magana kan irin halaccin da mahaifiyarsa ta yi wa Sanusi II wanda ko yan uwansa ba su yi masa ba.
'Abin da mahaifiyarmu ta yiwa Sanusi' - Sani Kwano
Sani Kwano bayyana irin jinya da mahaifiyarsa ta yi wa Sanusi II wanda yan uwansa ma ba su kula da shi kamar ita ba.
Ya ce:
"Babu dalilin mubaya'a kan abin da ba ra'ayinka ba, shi ya sani, ni na sani Sanusi II ba shi da gidan da ya wuce gidanmu a rayuwarsa.
"A shekaru 40 baya shi ya sani, mahaifiya ta babu hidimar da ba ta yi masa ba, ya yi rashin lafiyar da babu wani dan uwansa da ya zo, mahaifiya ta take kula da shi.
"Babu irin abincin da bai ci a gidan mu ba, riga ma ta yan uwana babu wacce bai ara ya sa ba shi Sanusi II."

Kara karanta wannan
Aminu Ado Bayero ya yi magana, ya faɗi abin da magoya bayansa suka yi a Fadar Sanusi II

Source: Twitter
An fadi yawan wadanda ke tare da Sanusi II
Kwano ya bayyana cewa suna yawa a gidan Sarki Sanusi II sun fi mutum 200 kuma ba dukansu ba ne ba su tare da shi akwai wadanda ke tare da shi.
"Akwai dan uwana Amadu, tare suke kwana a daki a baya, kuma Amadu yana tare da shi ba gaba dayanmu ba ne ba mu tare da shi."
- A cewar Sani Kwano
Sani Kwano ya ce a yau sun fi mutum 200 da yan uwansa a gidan Sarkin Kano kuma da yawa suna tare da shi Sarki Sanusi to ina ruwansa.
Ce-ce-ku-ce bayan korar wasu a fadar Sanusi II
Kun ji cewa daya daga cikin wadanda aka wulakanta a fadar Sarki Sanusi II ya ce har abada ba za su bar soyayya ga Aminu Ado Bayero ba.
Usman Sallama Dako ya koka kan yadda iyalansu ke fuskantar tozarci da rusau a gidan, yana zargin Sarki Sanusi da rashin adalci da tausayi.
Dako ya bayyana cewa shi bawan gidan masarauta ne, kuma zai cigaba da biyayya da kauna ga Aminu Ado duk da kaddarar rayuwa.
Asali: Legit.ng
