Amurka Ta yi wa Najeriya Martani bayan kin Karbar 'Yan Ciranin da Trump zai Turo
- Ofishin Jakadancin Amurka ya ce rage tsawon lokacin bizar da ya yi ba saboda sauye-sauyen da Najeriya ta yi ba ne
- Amurka ta ce hakan na zuwa ne yayin da kasar ke gudanar da sauye-sauyen tsarin bayar da biza a duniya baki ɗaya
- Haka zalika ofishin jakadancin ya ce matakin ba shi da alaka da rashin amincewar Najeriya wajen kin karbar 'yan cirani
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Amurka ya ce matakin da ya ɗauka na rage tsawon lokacin bizar Najeriya ba don nuna adawa da sauye-sauyen da Najeriya ta yi a hukumar shige da fice ba ne.
Tun daga shekarar 2023, ma’aikatar cikin gida a ƙarƙashin minista Olubunmi Tunji-Ojo ta fara aiwatar da sababbin tsare-tsare na zamani wajen bayar da biza da kula da shige da fice.

Source: Getty Images
A sakon da ta wallafa a X, Amurka ta kuma bayyana cewa matakin ba shi da alaka da kin karbar 'yan ciranin da shugaba Trump zai turo ko kuma shigar Najeriya BRICS.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangare na sauye-sauyen da Najeriya ta yi sun haɗa da cire tsarin samar da biza nan take, kafa sabon tsarin biza ta yanar gizo da sauransu.
Najeriya: Dalilin Amurka na rage lokacin biza
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Amurka ta bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin wani tsari na duba yadda ƙasashe ke amfani da bizar Amurka bisa wasu sharuɗan tsaro da fasaha.
Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Ba saboda matsayar kowace ƙasa ba ce kan batun 'yan cirani da aka ƙi karɓa daga Amurka, ko sabon tsarin shige da fice, ko kuma haɗin gwiwa da ƙungiyoyin kasashe irin su BRICS.”
Ta ƙara da cewa:
“Muna daraja alaƙar da muke da ita da Najeriya kuma muna fatan ci gaba da aiki tare da hukumomin ƙasar da jama’arta domin su cika sharuɗan da ake buƙata.”
Trump ya kakabawa Najeriya haraji
Bayan taron BRICS da Shugaba Bola Tinubu ya halarta a Brazil, Shugaban Amurka Donald Trump ya kakabawa kayayyakin Najeriya harajin kashi 10 cikin ɗari da ake shiga da su zuwa Amurka.
Wannan mataki da Trump ya ɗauka na daga cikin abubuwan da suka haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda dangantakar Najeriya da wasu ƙasashen Asiya ke ƙara ƙarfafuwa.
Matakin shugaban Amurka na kakaba haraji ba Najeriya kawai ya shafa ba, Donald Trump ya ce karin harajin zai shafi dukkan abokan huldar BRICS.

Source: Facebook
Najeriya ta zurfafa alaka da kasar Faransa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta amince da cigaba da kulla alaka mai kyau da Faransa a kan wasu muhimman abubuwa.
Karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Ojukwu ce ta bayyana haka yayin ganawa da Jakadan Faransa a Abuja.
Ministar ta ce Najeriya za ta cigaba da zurfafa alaka da Faransa a kan abubuwan da suka shafi ilimi, tsaro al'adu da sauransu.
Asali: Legit.ng

