Atiku, Ganduje, Saraki Barau Sun Taru a Auren Ɗan Tsohon Shugaban Ƙasa a Abuja
- Fitattun 'yan Najeriya sun taru a Babban Masallacin Abuja domin shaida daurin auren Musa Yar’Adua da Maryam Ayuba bayan sallar Juma’a
- Daga cikin manyan baki akwai dangin marigayin shugaban ƙasa Umaru Yar’Adua da sauran abokai da ‘yan siyasa masu mutunci da dangantaka da iyalan
- An yi addu'a da roƙon Allah ya ba sababbin ma’auratan hikima da haƙuri domin gina gida mai cike da farin ciki da fahimtar juna
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - A yau Juma’a, 11 ga Yuli, manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun taru a babban masallacin birnin tarayya da ke Abuja.
Hakan ya biyo bayan daura auren auren Musa Umaru Yar’Adua, ɗan marigayi Shugaban Ƙasa, Umaru Musa Yar’Adua, da Amaryarsa, Maryam Ayuba Shuaibu.

Source: Facebook
Manyan jiga-jigai da suka taru a daurin aure
Hakan na cikin wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya wallafa a shafin X a daren yau Juma'a 11 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da daurin auren ne bayan kammala Sallar Juma’a, inda aka shaida fitattun mutane daga siyasa, addini da al’adun gargajiya da suka halarta tare da iyalai da abokai.
Atiku na daga cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren ya wanda ya bayyana cewa akwai zumunci mai karfi tsakaninsa da iyalan Yar’Adua tun da dadewa.

Source: Depositphotos
Atiku ya yabawa tarbiyyar gidan marigayi Yar'adua
Atiku ya bayyana cewa sababbin ma’auratan sun fito daga gida mai cike da tarbiyya da mutunci, kuma sun gaji ginshikan al’ada da tsantsar addini a rayuwarsu.
Daurin auren ya kasance taron farin ciki da addu’o’i, inda mahalarta suka roƙi Allah ya ba Musa da Maryam haƙuri, hikima da fahimtar juna.
An jaddada cewa wannan aure zai zama tushe na gina gida mai albarka da cike da zaman lafiya da ƙaunar juna a tsakanin ma’auratan.
Manyan baki da suka halarci daurin auren
Sauran wadansa suka halarci daurin auren akwai tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda Bola Tinubu ya sake nada shi mukami a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
Littafi: Garba Shehu ya tara Gowon, Atiku, Osinbajo, El Rufa'i, Aminu Ado a Abuja
Sauran wadanda suka halarci daurin auren akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da tsohon gwamnan Kwara kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.
Har ila yau, akwai manyan yan siyasa da yan kasuwa wadanda suka samu halartar daurin auren domin sanya albarka ga yayan marigayin.
Kwankwaso, El-Rufai da jiga-jigai sun hadu a Abuja
Kun ji cewa tsohon Antoni-Janar na tarayya, Mohammed Bello Adoke ya kaddamar da littafinsa a birnin tarayya Abuja a wannan mako da muke ciki.
Shahararrun ‘yan siyasa da suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Mohammed A doke ya bayyana cewa ya yafewa duk wanda ke da hannu a shari’ar da ta bata masa suna dangane da OPL245 lokacin mulkin Muhammadu Buhari a Najeriya.
Asali: Legit.ng
