Kungiyar Musulmi Ta Bayyana Gwamnan da Zai Iya Zama Shugaban Ƙasa a Najeriya

Kungiyar Musulmi Ta Bayyana Gwamnan da Zai Iya Zama Shugaban Ƙasa a Najeriya

  • Ƙungiyar kare haƙƙin musulmin Najeriya, MURIC ta bukaci ’yan Najeriya su gujewa nuna bambanci tare da mu’amala da juna bisa gaskiya da soyayya
  • MURIC ta yaba wa Gwamnan Anambra, Charles Soludo, tana mai cewa yana da halayen da suka dace da wanda zai iya shugabancin Najeriya nan gaba kadan
  • Ƙungiyar da ke fafutukar kare gaskiya bisa tsarin addinin musulunci ta jaddada cewa sai an cire ƙabilanci sannan Najeriya za ta samu waraka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta yaba wa gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo bisa abin da ta kira “wanke Fulani daga zargi.”

Tun farko dai Gwamna Soludo ya fito ya wanke Fulani makiyaya daga zargin da ake masu na kai hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane a Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola.
Kungiyar MURIC ta ce Gwamna Soludo zai iya zama shugaban ƙasa nan gaba Hoto: @TIBMovement
Source: Twitter

Gwamna Soludo ya wanke fulani daga zargi

Gwamnan ya bayyana cewa mafi yawan waɗannan abubuwa na rashin tsaro da ke faruwa a Anambra da jihohin Kudu maso Gabas ba Fulani ke aikata su ba, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wasu miyagun mutane daga cikin 'yan kabilar Igbo da suka fi ya a yankin ne aikata wannan ta'asa da ta ƙi ci kuma ta ƙi cinyewa.

MURIC, ƙungiyar addinin Musuluncu a Najeriya, ta jinjinawa gwamnan bisa wannan gaskiyar da ya faɗa ba tare da fargabar komai ba.

Wane gwamna ake ganin zai shugabanci Najeriya?

Kungiyar ta kuma bayyana Soludo a matsayin wanda ke da halayen shugabanci da suka dace da wanda zai iya zama shugaban Najeriya a nan gaba.

MURIC ta faɗi haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, 11 ga Yuli, ta hannun shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola, wadda ta shiga hannun Legit Hausa.

Kara karanta wannan

Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa

A sanaewar MURIC ta ce:

"Gaskiya ta yi halinta, yanzu duk masu bibiyar abubuwan ɓarna da sace-sacen mutane da kashe-kashen da ke faruwa a Kudu maso Gabas ya san ainihin abin da ke faruwa.
"Muna mika godiya ga Gwamna Soludo bisa wannan gaskiya da ya bayyana, ya nuna jajircewa da jarumta matuƙa.
“Wannan faɗar gaskiya ba tare da la’akari da wanda za ta shafa ba, Soludo ya tabbatar da cewa lallai shi shugaban ƙasa ne da Najeriya ke jira.”

MURIC ta shawarci gwamnoni su yi koyi

Kungiyar ta nanata cewa laifi kowane iri ne kuma a ko'ina ake aikata shi, ba ya da alaƙa da ƙabila ko addini.

Ta kuma bukaci sauran gwamnoni, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma a yankin Kudu maso Gabas da su yi koyi da Gwamna Soludo ta hanyar faɗar gaskiya kan wannan batu.

Gwamnan Anambra, Charles Soludo.
MURIC ta kwararo yabo ga Gwamna Soludo na jihar Anambra Hoto: Charles Soludo
Source: Facebook

Maimakon su nuna fushi da ɓacin rai kan maganar Soludo, MURIC ta bukaci mutanen Igbo da su goya masa baya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya wanke Fulani, ya fadi masu kai hare hare a jiharsa

MURIC ta ce:

“Wannan alama ce da ke nuna yana da halayen zama shugaban ƙasa nan gaba, wanda ya kamata ’yan Igbo su tallafa masa har ya kai ga nasara.
"A wurin mu, duk wanda zai iya rungumar kowa daga kowane yanki da addini ba tare da nuna banbanci ba, mutum ne mai daraja, Soludo yana da ƙima da mutunci."

Da gaske Gwamna Soludo ya je wurin boka?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Charles Chukwuma Soludo na Anambra ya musanta zargin.cewa ya garzaya wurin wani boka don neman nasara a zaɓe mai zuwa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra a watan Nuwambar 2025.

Gwamnatin Charles Soludo ta ce bidiyon da ke yawo yana nuna wai Gwamna yana magana da boka, an ɗauke shi ne a wurin taro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262