Kotu Ta Raba Gardama kan Karar da Abba Hikima Ya Shigar da Wike a Abuja
- Babbar kotun tarayya ta kori karar da wasu marasa galihu suka shigar suna neman Naira miliyan 500 daga Nyesom Wike bisa cin zarafinsu
- Alkalin kotun ya ce shaidar da masu karar suka gabatar ba ta da inganci, kuma rahoton jarida ba hujja ba ce bisa doka
- Kotun ta ce gwamnati tana da ikon korarsu daga titunan Abuja saboda lafiyar jama'a da kiyaye tsaftar muhalli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta yi zama tare da yanke hukunci kan karar da aka shigar da Nyesom Wike.
Kotun ta kori karar da wasu marasa galihu suka shigar suna zargin Minista Wike da take musu hakkokinsu.

Source: Facebook
Wadanda suka shigar da Wike kara a kotu
Alkalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya ce karar ba ta da inganci domin babu wata hujja da ke nuna an tauye musu hakkokin da doka ta tanada, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu karar sun hada da ‘yan talla, almajirai da masu bola jari wadanda suka nemi kotu ta basu diyya na N500m.
Lauyansu Abba Hikima ya ce an kama su ba bisa ka’ida ba, an tsare su ba tare da tuhuma ba, sannan an ci zarafinsu.
Sai dai alkalin ya ce rahotannin da suka danganta da jaridu ba za a amince da su ba idan ba su da sahalewar doka.
'Gwamnati na da hurimin dakile matsalar tsaro' - Kotu
Kotun ta kara da cewa babu wani jami’in gwamnati da aka ambata da sunan wanda ya aikata tauye hakkin da ake korafi a kansa.
Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa gwamnati na da hakkin dakile ayyukan da ke barazana ga lafiyar jama’a da tsarin gari.
Ya ce wadanda ke karar da almajirai na cutar da lafiyar jama’a saboda kazanta da su ke haifarwa da kuma yiwuwar barazana ga tsaro.

Source: Facebook
Dalilin korar karar Hikima da kotu ta yi
Kotun ta ce gwamnati ta samar da cibiyoyi na koyon sana’a a Bwari don horar da su, amma sun ki amfana da damar.
Alkalin ya kara da cewa ba da wannan diyya zai bude hanyar almundahana da kudin jama’a a hannun wasu da ba su da nasaba da karar.
Ya bayyana cewa rokon kudin diyya babu wani bayani ko sunan wadanda za a raba musu kudin, wanda ya sa shari’ar ta gaza, cewar News Agency of Nigeria.
A karshe, kotun ta kori karar gaba daya bisa rashin hujjoji da kuma rashin ingancin bayyanar da tauye hakki da ake zargi.
Wike ya umarci fatattakar mabarata a Abuja
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da sabon shiri a Abuja don kawar da dukkanin masu karamin karfi da bara daga birnin.
An kafa kwamitin hadin gwiwa da jami’an tsaro don aiwatar da umarnin, inda za a rika zagayawa domin cafke wadanda ake zargi.
A cewar Wike, wannan shiri ya biyo bayan bukatar da ake da shi na kawata Abuja a matsayin babban birnin kasar.
Asali: Legit.ng

