Dangote Ya Bayyana Shakku kan Matatun Man Gwamnati bayan Kashe Biliyoyin Daloli

Dangote Ya Bayyana Shakku kan Matatun Man Gwamnati bayan Kashe Biliyoyin Daloli

  • Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya nuna damuwa kan rashin farfaɗo da matatun gwamnatin tarayya
  • Ya ce zai yi wahala matatun gwamnati su dawo da cikakken aiki, duk da kashe sama da dala biliyan 18 wajen gyaransu
  • Dangote, ya kara da bayyana yadda ya taba sayen matatun kasar nan, amma da aka samu sauyin gwamnati, aka kwace

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Shugaban rukunin kamfanin Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shakku da damuwa kan yiwuwar gyara matatun mai na gwamnatin tarayya.

Dangote ya bayyana wannan ne duk da cewa an kashe sama da Dala biliyan 18 wajen gyaran matatun da ke Fatakwal, Warri da jihar Kaduna.

Alhaji Aliko Dangote
Dangote ya na shakku kan matatun Najeriya Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Dangote ya ce tsofaffin kayan aiki da matsalolin tafiyar da su yadda ya kamata ne suka sa ya yi imani cewa matatun ba za su dawo da cikakken aiki ba har abada.

Kara karanta wannan

Jonathan ya zargi Buhari da gallazawa jami'ansa kan badakalar Malabu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya taba ‘sayen’ matatun mai

Jaridar Punch News ta ruwaito cewa Dangote ya ce kamfaninsa ya taɓa sayen matatun man na gwamnati a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Alhaji Aliko Dangote
Dangote ya fadi matsalar matatun Najeriya Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Ya kara da cewa amma bayan an samu sauyin gwamnati ne aka tilasta masa ya mayar da su bayan an shaidawa gwamanti bayanan cewa akwai buƙatar a maido su.

Dangote ya kara da bayyana cewa:

“Mun sayi matatun a watan Janairu 2007. A wancan lokacin, matatun na samar da kimanin 22% na man fetur. Amma da gwamnati ta canza, aka bukaci mu mayar da su ga gwamnati.”

A cewarsa, wasu jami’an gwamnati ne a lokacin suka shawo kan marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua cewa kamfanin NNPCL zai iya tafiyar da kansu.

Dangote ya fadi dalilin gina matatarsa

Aliko Dangote ya bayyana cewa ƙin sayar masa da matatun man gwamnatin Najeriya ne ya haifar da tunanin gina matatarsa domin cimma burinsa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da ke hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara

Dangote, ya gina matatar mai mai zaman kanta da ke da karfin tace gangar danyen mai 650,000 a kowacce rana a jihar Legas.

Yanzu dai ana sa ran wannan matatar Dangote za ta taimaka matuka wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje da karancinsa.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ma ya taba bayyana irin matsalolin cin hanci da rashin iya tafiyar da matatun a matsayin babbar matsala da ta sa su gaza aiki.

Dangote ya rubutawa Tinubu wasika

A wani labarin, mun wallafa cewa Aliko Dangote, ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan matakan da yake ɗauka don bunƙasa ayyukan raya ƙasa.

A wata budaddiyar wasiƙa da Dangote ya aike wa shugaban ƙasar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na aiki tukuru wajen rage haɗarin ambaliya a jihar Legas.

Ya kuma bayyana cewa ayyukan titunan tarayya da ake aiwatarwa a fadin ƙasar na daga cikin manyan abubuwan da suka cancanci yabo a gwamnatin Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng