Ruwan Sama: An Shiga Matsala Mai Girma a Kano, Malamai Sun Buƙaci a Fito Sallah

Ruwan Sama: An Shiga Matsala Mai Girma a Kano, Malamai Sun Buƙaci a Fito Sallah

  • Malaman addinin Musulunci a jihar Kano sun bukaci ɗaukacin al'umma su fita sallar rokon ruwa sakamakon ƙarancin ruwan da ake fama da shi
  • Shugaban Majalisar malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu
  • Ya buƙaci musulmi su fito sallar rokon ruwa gobe Asabar da misalin ƙarfe 9:00 domin neman taimakon Allah a daminar bana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Yayin da daminar bana ta kankama, an fara shiga yanayin ƙarancin ruwan sama a wasu sassan jihar Kano bayan manoma sun fara harkokinsu na noma.

Wannan dai ba karamar matsala ba ce ga manoma da sauran al'umma a lokacin damina, malamai sun buƙaci a fito sallar rokon ruwa domin neman taimakon Allah.

An fara ƙarancin ruwa a daminar bana a Kano.
Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta shirya sallar rokon ruwa a Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

A rahoton da Leadership ta wallafa, Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta jihar Kano, ta bukaci mutane su fito roƙon ruwa daga gobe Asabar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace malamin addinin musulunci, sun bukaci N30m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman Kano sun buƙaci a fito rokon ruwa

Shugaban Majalisar malamai na Kano, Sheikh Ibrahim Ƙhalil ya buƙaci musulmai su fito sallar roƙon ruwa saboda ƙarancin ruwan sama da ake fama da shi yayin da damina ke ƙara nisa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Majalisar Malaman Kano ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sheikh Ibrahim Khalil yau Juma'a, 11 ga watan Yuli, 2025.

Shugaban Majalisar, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce an yanke shawarar gudanar da sallar ne sakamakon ƙarancin ruwan sama da ake fuskanta a bana.

An sa lokacin sallahr rokon ruwa a Kano

Ya ce an shirya gudanar da sallar roƙon ruwan ne a ranar Asabar, 12 ga Yuli, da karfe 9:00 na safe, a masallacin Jumu’a na Umar Bin Khattab da ke kan titin Zaria.

Majalisar ta bukaci jama’a da su halarta da ikhlasi da hadin kai, suna neman rahama da albarkar Allah domin a samu saukin yanayi da isasshen ruwan sama.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulmi ta bayyana gwamnan da zai iya zama shugaban ƙasa a Najeriya

"A madadin Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta ƙasa reshen jihar Kano, muna gayyatar al'umma baki ɗaya zuwa wurin sallar rokon ruwa.
"Za a yi wannan sallah ne domin neman taimakon Allah sakamakon ƙarancin ruwan sama da ake fama da shi duk da damina ta fara nisa."
"Za a gudanar da sallar rokon ruwan ne a gobe Asabar, 12ga watan Yuli, 2025 da misalin ƙarfe 9:00 na safiya a masallacin Umar bn Kattaɓ da ke kan titin Zaria a Kano."

- In ji Sheikh Ibrahim Khalil.

Shugaban Majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel.
An shirya sallar rokon ruwa ranar Asabar a Kano Hoto: Sheikh Ibrahim Khaleel
Source: Facebook

Daga karshe, malamin ya yi addu'ar Allah Ya karɓi ibadun musulmi kuma ya sa wa daminar bana albarka.

Malam Abdullahi Yahuza ya shaida wa Legit Hasua cewa wannan matsalar ta ƙarancin ruwan sama a damina ba Kano kaɗai ta shafa ba.

A cewarsa, fita rokon ruwa ita ce mafita da Allah Ya zaɓa wa musulmi a duk lokacin da irin haka ta faru, sai dai ya roki mutane su gyara halayensu.

"Matsalar ƙarancin ruwa ba Kano kaɗai ke fama da ita ba, mu kanmu a nan Ɗanja mun yi kwana uku muna fita rokon ruwa kafin mu samu ruwan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Nasarawa, an samu asarar rai

"A zahirin gaskiya dole mutane su gyara halayensu, laifukan da ake aikatawa kare ma ba zai ci ba, taya zamu zauna lafiya, taya zamu samu ruwa? Dole mu tubar ma Allah."

Za a yi mamakon ruwan sama a jihohin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci tsawa, ruwan sama da iska mai ƙarfi Arewa da yankin Kudu.

A cikin rahoton, NiMet ta yi hasashen cewa yawancin sassan Najeriya za su samu ruwan sama mai yawa tare da tsawa da iska mai ƙarfi a ranar Alhamis.

Sanarwar hasashen yanayin, wacce NiMet ta fitar a ranar 9 ga Yulin 2025, ta bayyana cikakken yanayin ruwa da ake sa ran samu a jihohin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262