Aminu vs Sanusi: Rikicin Sarautar Kano na Neman Dawowa Ɗanye, An Aika Saƙo ga Kotun Ƙoli
- Wata ƙungiya ta roki kotun kolin Najeriya ta gaggauta yanke hukuncin da zai kawo ƙarshen rikicin sarautar Kano da ake fama da shi
- A wani taron manema labarai, shugabannin ƙungiyar sun ce idan aka ci gaba da jinkiri, lamarin na iya shafar yanayin tsaro a Kano
- Sarakunan Kano, Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, kowane na kiran kansa sarkin Kano tun bayan gyara dokar masarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Wata ƙungiya ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi masanan siyasa, masu rajin kare dimokuraɗiyya, da yaƙi da rashin nagartaccen shugabanci ta dawo da batun shari'ar sarautar Kano.
Ta bukaci Kotun Koli ta gaggauta yanke hukunci kan rikicin masarautar Kano da ke ci gaba da ɗaukar lokaci, tana gargaɗin cewa jinkiri zai iya haifar da rikici a jihar.

Source: Facebook
Ƙungiyar mai suna Coalition of Political Analysts Forum, Democracy Protectors and Good Governance, ta bayyana haka ne a taron manema labarai a Kano, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rikicin sarautar Kano ya samo asali
Kano na fama da rikicin sarauta ne tun bayan dawo da Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Abba Kabir ta yi, tare da rusa masarautu biyar da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya ƙirƙiro.
Sai dai duk da tsige shi daga sarauta, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ci gaba da ayyana kansa a matsayin sarki tare da zama a Fadar Nasarawa, lamarin da ya kai gaban kotu.
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan dogon lokacin da shari’ar ke ɗauka da yadda hakan ke jefa al’ummar jihar Kano cikin rudani da rashin tabbas a siyasa da al’adu.
An roki kotun koli ta warware rikicin Kano
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Al-Amin Albarra, da Sakatare, Malam Saminu Abubakar, sun roƙi kotun koli da ta kawo ƙarshen wannan rikici na sarautar Kano.

Kara karanta wannan
Aminu Ado Bayero ya yi magana, ya faɗi abin da magoya bayansa suka yi a Fadar Sanusi II
Sun buƙaci kotun ta yi bayani game da tanadin kundin tsarin mulki kan yadda ake kafa, sake tsara da sahihancin sarakuna a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
A cewarsu:
“Wannan rikici yana da nasaba da kundin tsarin mulki, kuma yana buƙatar hukunci mai ƙarfi da bayani daga Kotun Koli.”

Source: Twitter
Rikicin sarauta ya raba kan mutanen Kano
Ƙungiyar ta bayyana cewa rikicin Aminu Ado da Sanusi II ya raba kan jama’ar Kano tun daga siyasa da biyayya ga masarauta, wanda hakan ke ƙara dagula yanayin zamantakewa.
Ta yi gargaɗi cewa idan aka cigaba da jinkirta yanke hukunci, lamarin na iya rikidewa zuwa babban rikicin da zai taɓa tsaro, musamman ganin irin rawar da masarautun gargajiya ke takawa a Arewacin Najeriya.
“Hukuncin kotu ba wai kawai zai kawo bayani daga mahangar doka ba ne, har ma zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya, ƙarfafa haɗin kai da hana rikice-rikicen da za su iya tasowa daga irin wannan rikici a gaba."
Aminu Ado ya musanta zargin da ake masa
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya musanta zargin da ake cewa magoya bayansa ne suka fara tayar da rikici a Fadar Ƙofar Kudu.

Kara karanta wannan
Harin da aka kai Fadar Sarki Muhammdu Sanusi II ya ƙara tayar da ƙura a jihar Kano
Alhaji Aminu Ado, wanda gwamnatin Kano ta tube daga sarauta, ya ce magoya bayansa sun yi kokarin kare kansu ne a lokacin da aka tare su.
Mai taimaka wa Sarki Bayero kan harkokin yaɗa labarai, Khalid Uba, ya shaida wa manema labarai cewa babu makamai a hannun magoya bayan Aminu Ado.
Asali: Legit.ng
