Tinubu Ya Fara Bugawa da Trump kan Kawo 'Yan Ciranin Amurka Najeriya

Tinubu Ya Fara Bugawa da Trump kan Kawo 'Yan Ciranin Amurka Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta karɓi ‘yan Venezuela da Amurka ke shirin mayarwa ba, musamman wadanda ke cikin kurkuku
  • Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na fama da nata matsalolin da ba za ta karbi na wasu kasashe ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa Najeriya na tattaunawa da Amurka kan sabon kalubalen biza da kuma nuna damuwa kan hana biza daga UAE

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta amince da matsin lambar gwamnatin Donald Trump na Amurka domin karɓar 'yan Venezuela da za a kora daga kasar ba.

Najeriya ta nuna kin amincewa da bukatar Trump ta turo 'yan cirani musamman wadanda suka fito daga kurkukun Amurka.

Kara karanta wannan

Najeriya da Faransa za su zurfafa alaka da juna kan tsaro da abubuwa 3

Najeriya ta ki yarda da bukatar Trump ta kawo 'yan ciranin Amurka
Najeriya ta ki yarda da bukatar Trump ta kawo 'yan ciranin Amurka. Hoto: Donald J Trump|Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a wani shirin na Channels TV a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuggar ya ce Najeriya na da nata kalubalen da take fama da su kuma ba za ta zama wurin ajiye fursunonin wata kasa ba, musamman a wannan lokaci da kasar ke da jama'a fiye da miliyan 230.

'Ba za mu zama mafakar fursunoni ba,' Najeriya

Tuggar ya bayyana cewa Najeriya ba za ta rungumi shirin da wasu kasashen ke yi na kokarin mayar da wasu ‘yan gudun hijira ko fursunoni daga kasashen waje ba.

Tribune ta wallafa cewa Tuggar ya ce:

“Za a iya cewa Amurka na matsa lamba ga kasashen Afirka da su karɓi wasu ‘yan Venezuela da suke shirin korar su, ciki har da wadanda ke fitowa daga gidajen yari.
"Wannan ba abu ne da zai yiwu ba.”

Kara karanta wannan

'Mun gane wayon': ADC ta yi martani kan zargin shiryawa Tinubu 'juyin mulki'

Ministan ya ce Najeriya na da nauyin da ke kanta na kula da tsaro, tattalin arziki da walwalar jama’ar ta, don haka ba za ta yarda ta zama wurin kwashe matsalolin wasu kasashe ba.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar. Hoto: Federal Ministry of Foreign Affairs
Source: Twitter

Ziyarar Tinubu a BRICS da martanin Trump

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya halarci taron kolin BRICS da aka gudanar a Rio de Janeiro, Brazil, daga 6 zuwa 7 ga watan Yuli, 2025.

A rana ta ƙarshe ta taron, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai ƙara harajin kasuwanci da kashi 10 cikin 100 kan kasashen BRICS da ya kira “masu adawa da Amurka.”

Sai dai Tuggar ya ce,:

“Batun karin haraji da Trump ke yi ba lallai ne ya shafi halartar Najeriya a taron BRICS ba. Wannan na iya kasancewa bangare ne na manufofin kasuwancin Amurka.”

Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da gwamnatin Amurka kan sabon tsarin biza da ya takaita lokacin zaman ‘yan Najeriya a Amurka.

Najeriya ta kuma bayyana takaici kan matakin da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta dauka na hana wasu ‘yan Najeriya biza.

Najeriya za ta zurfafa alaka da Faransa

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Dala miliyan 747 domin aikin titi a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya za ta zurfafa alaka da kasar Faransa kan wasu muhimman abubuwa.

Legit Hausa ta gano haka ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin karamar ministar harkokin wajen Najeriya da jakadan Faransa.

Ambasadan Faransa ya bayyana cewa za su shirya wani taron kwana biyu da ya shafi kasasen Afrika a Legas a nan gaba kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng