Najeriya da Faransa za Su Zurfafa Alaka da Juna kan Tsaro da Abubuwa 3

Najeriya da Faransa za Su Zurfafa Alaka da Juna kan Tsaro da Abubuwa 3

  • Najeriya da Faransa sun amince da zurfafa dangantakarsu a fannoni da suka hada da kasuwanci, al’adu, ilimi da tsaro
  • Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Ojukwu, ta gana da jakadan Faransa a Najeriya, Marc Fonbaustier
  • An bayyana shirye-shiryen gudanar da bikin tunawa da Fela Kuti da taron “Creation Africa” a Legas daga 16 zuwa 18 ga Oktoba, 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Abuja - Najeriya da gwamnatin Faransa sun amince da kara zurfafa hadin gwiwa a bangarori da dama, ciki har da kasuwanci, tsaro, ilimi da kuma al’adu.

Wannan na cikin sakamakon wata muhimmiyar ganawa da ta gudana tsakanin Najeriya da Faransa.

Ministar harkokin wajen Najeriya tare da ambasan Faransa
Ministar harkokin wajen Najeriya tare da ambasan Faransa. Hoto: @NTANewsnow
Source: Twitter

Tashar NTA ta wallafa a X cewa ministar harkokin wajen Najeriya mai kula da harkokin kasashen waje, Bianca Ojukwu ta gana da jakadan Faransa a Najeriya, Marc Fonbaustier.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ojukwu ta nemi karin hadaka da Faransa

A yayin ganawar, Ojukwu ta jaddada cewa Najeriya a shirye take ta aiwatar da yarjejeniyoyin da Shugaba Tinubu ya cimma da kasar Faransa a ziyararsa ta shekarar 2024.

A shekarar da ta wuce shugaban Najeriya ya ziyarci kasar Faransa, kuma sun kulla yarjejeniya kan hakar ma'adinai.

Ana fatan yarjejeniyar da Faransa ta kulla da Najeriya za ta jawo habaka tattalin arzikin Najeriya ta fannoni da dama.

Faransa za ta shirya biki na musamman a Najeriya

Jakadan Faransa, Marc Fonbaustier, ya bayyana cewa akwai sababbin shirye-shiryen al’adu da za su kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Ya bayyana cewa daga cikin shirye-shiryen akwai wani bikin nune-nunen tarihin mawakin Najeriya, Fela Anikulapo Kuti, wanda za a yi a Najeriya.

Haka zalika, za a gudanar da babban taron "Forum Creation Africa" a Legas daga 16 zuwa 18 ga watan Oktoba, 2025, domin hadin gwiwar al’adu a nahiyar.

Kara karanta wannan

Najeriya ta samu tallafi mai yawa daga Faransa, za a yi aiki a Katsina, sauran jihohi

Bola Tinubu da shugaban Faransa
Bola Tinubu da shugaban kasar Faransa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Faransa ta yabawa sauye-sauyen Najeriya

Fonbaustier ya yabawa gwamnatin Shugaba Tinubu bisa sauye-sauyen tattalin arzikin da take yi da nufin jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.

A karshe, jakadan ya gayyaci Bianca Ojukwu da ta halarci bikin Ranar Kasa ta Faransa da za a gudanar a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuli, 2025.

Rahoton VON ya ce jakadan ya ce irin wannan hadin gwiwar tsakanin Faransa da Najeriya zai taimaka wajen bunkasa ci gaba da fahimta a tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

Tun bayan zuwan Bola Tinubu mulki a 2023 shugaban kasar ke kokarin kulla alaka mai kyau tsakanin kasashen biyu.

Faransa za ta tallafawa Najeriya da kudi

A wani rahoton, Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin Faransa ta yarda da tallafawa Najeriya da makudan kudi domin ayyukan habaka tattali a dukkan jihohin kasar da FCT, Abuja.

Ministar al'adun Najeriya, Hannatu Musawa ce ta bayyana hakan wa manema labarai inda ta ce za a yi amfani da kudin da Faransa ta bayar wajen gina cibiyoyin fasaha a Najeriya.

Hannatu Musawa ta kara da cewa a karon farko za a fara kafa cibiyoyin a jihohin Katsina, Legas da Abuja kafin daga bisa a samar da su a sauran jihohin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng