Tinubu Ya Tura Shettima London Duba Lafiyar Buhari da ke Kwance a Asibiti

Tinubu Ya Tura Shettima London Duba Lafiyar Buhari da ke Kwance a Asibiti

  • Shugaba Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa da ya je London domin duba tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke jinya
  • Rahotanni sun ce Buhari na karbar magani a asibiti da ba a bayyana ba a birnin London, Kashim Shettima ya isar masa da sakon Tinubu
  • Rahotanni sun nuna cewa Muhammadu Buhari na cikin kulawa amma ba cikin mawuyacin hali yake ba, kuma yana samun sauƙi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, zuwa birnin London domin duba tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke jinya a wani asibiti.

Shettima ya kai ziyarar ne daga Addis Ababa, Habasha, inda ya halarci kaddamar da shirin gwamnatin Habasha a karshen mako, bisa gayyatar Firayim Minista Abiy Ahmed.

Kara karanta wannan

An hango Kashim Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki tare a Abuja

Shettima ya ce duba Buhari a asibitin London
Shettima ya ce duba Buhari a asibitin London. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Wata majiya ta bayyana wa Daily Trust cewa shugaba Tinubu ya bada wannan umarni ne bayan samun labarin cewa Buhari yana asibiti yana jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya na jinya amma ba cikin ICU ba

Rahotanni sun ce Buhari ya kamu da rashin lafiya kuma yana jinya a wani asibiti a London, lamarin da ya jawo damuwa daga ‘yan Najeriya.

Sai dai tsohon hadimin Buhari a fannin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa ba cikin ICU yake ba, yana samun sauki.

A cewarsa:

“Gaskiya ne cewa Buhari na jinya kuma yana samun kulawa, amma ba kamar yadda ake yada labarin yana cikin matsanancin hali ba.
"Yana samun sauƙi sosai kuma muna fata zai warke da wuri.”

Shettima ya kai ziyarar sirri a wajen Buhari

A cewar majiyar, Shettima ya sauka a London da sassafe ranar Litinin kuma ya shafe sa'o'i tare da Buhari yana masa jaje da isar da sakon Tinubu.

Kara karanta wannan

Littafi: Garba Shehu ya tara Gowon, Atiku, Osinbajo, El Rufa'i, Aminu Ado a Abuja

Majiyar ta ce bayan tattaunawa, Shettima ya hada Buhari da Tinubu a waya kafin ya tashi daga asibitin.

Haka kuma, an bayyana cewa Shettima ya kai ziyara ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda shima yana jinya a London a lokacin.

Ba a bayyanawa jama’a dalilin ziyarar ba

Lokacin da wakilin Arise News ya tuntubi hadimin Shettima a fannin yada labarai, Stanley Nkwocha, sai ya ce ziyarar ta kasance ce ta sirri.

Nkwocha ya ce:

“Gaskiya ne Shettima ya je London, amma ba zan iya tabbatar da cewa ya ziyarci Buhari ko Abdulsalami ba. Ziyara ce ta sirri kuma ban san irin ayyukan da ya yi a can ba.”

Stanley Nkwocha ya kara da cewa Shettima ya dawo Najeriya daga London a ranar Litinin da ta gabata.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha zuwa London lokacin da yake mulki domin neman lafiya, ciki har da wata jinya da ta dauki kwana 104.

Lafiyar Buhari ta kasance daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Tsaro: Nuhu Ribadu ya ba Tinubu kariya, ya gargadi 'yan adawan Najeriya

Shugaba Tinubu tare da Muhammadu Buhari
Shugaba Tinubu tare da Muhammadu Buhari. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mutanen Buhari da Tinubu na cacar baki

A wani rahoton, kun ji cewa mutanen shugaba Muhammadu Buhari da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun fara musayar yawu.

Alakar magoya bayan 'yan siyasar ta fara tsami ne bayan an fara takaddama kan ko Bola Tinubu ne ya jawo nasarar Buhari a 2015.

Tsohuwar hadimar shugaba Buhari, Lauretta Onochie ta yi ikirarin cewa tun a karon farko Bola Tinubu bai goyi bayan Buhari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng